Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

TARIHIN KANO KASHI NA DAYA

$
0
0

Kafin mu shiga tarihin Kano kai tsaye, yana da kyau mu fara nazari akan asalin Hausawa wadanda sune su ka kafa mulki a Kano.

Gano asalin Hausawa babban abu ne, domin nema yake ya buwayi masu bincike da nazari. Masana a aji da matakai daban-daban sun zo da bayanai mabanbanta a kan asalin Hausawa, amman har zuwa yau an rasa wani tartibin zance da za a ce an dauka a matsayin sahihi. Ma su duba siffar harshe sun bada na su bayanin, suma ma su tafsirin al’adu sun ba da na su, amman duk an kasa cimma matsaya daya.

Rubutaccen tarihin Hausa da aka samu a gun su Hausawan yana alakanta asalin su da wani mutum da ake kira Bayajidda. Ta kai da an ce asalin Bahaushe, abin da ke fara zuwa zuciya shi ne; Bayajidda.

Bayajidda dai kamar yadda Masana suka rawaito, mutumin kasar Bagadaza ne da ya zo kasar Hausa ta yankin Borno. Ya zo Daura har ma ya Auri Sarauniya Daurama kuma ta haifa masa yaya bakwai, sannan baiwar ta da ta bashi ita ma ta haifa masa yaya guda bakwai. Idan muka dubi wannan labari da kyau zamu fahimci akwai tambayoyi biyu da suke bukatar amsa. Ta daya, idan Bayajidda ne asalin Hausawa, su mutanen da sarauniyar da da ya tarar Al’janu ne? Ta biyu, shin da ya zo, Bebaye ne su ko kurame?

Wasu masanan da suka tabbatar da cewa wannan batun ba shi da tushe, sun bada bayanin cewa shi Bayajidda shi ne asalin mulki a kasar Hausa ba wai asalin Hausawa ko harshen su ba. Sun dogara da cewa; tunda yankin da ya fito yanki ne da yake da wayewa ta mulki, ta yiwu shi ya kawo wa Hausawa irin tsarin Sarki da suke da shi yanzu. Raunin wannan ruwaya ita ma shi ne tilista dangantaka tsakanin Hausawa da Larabawa wadda alama ce ta tasirin Musulunci.

Na biyu, sabbin hujjojin kimiyya sun nuna cewa kasar Hausa ta riga garin Bagadaza kafuwa da akalla shekaru dari bakwai! Tirkashi! Wasu kuma sun dau ma’anar cewa gaba daya ma labarin hikima ce da dabara ta mutanen da.

Wadannan Ajin na Masana, sun fassara Bayajidda da cewa Muslunci ne, micijiyar da ya kashe kuma maguzanci, Auren sa da Sarauniyar kuma a matsayin fahimta da imani da masu mulkin kasar Hausa suka samu da sabon addinin Musulunci da ya zo musu daga Gabas. Itama wanna magana tana da rauni kasancewar kasar Hausa ta gabaci zuwan Annabi Muhammdu da shekaru akalla dari biyar!

Magana ta karshe da zamu duba ta asalin Hausawan ita ce; wacce take cewa su Hausawa asalin su mutanen Habasha ne da suka yi hijjra zuwa kasar Hausa. Ai ance ita kanta kalmar Bahaushe ma gurbataccen furucin kalmar Bahabashe ce.

Don neman Karin bayani, tuntubi: Arabiandokaji@gmail.com ko 08135353532

The post TARIHIN KANO KASHI NA DAYA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>