Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

ALFAWA’ID NA (ABUBUWAN DA ZAMU FA’IDANTU DA SU) KASHI NA UKU

$
0
0

 

Shehun Malami Abdurrahman dan Nasir Assi’id Allah ya yi masa rahama ya ce:”Abin da yake nuna Bawa mai rabauta ne a wajen Allah shi ne; Iklasinsa ga Allah da kuma kai-kawo dinsa wajen amfanar da bayin Allah. Kamar yadda rashinsu yake nuna tabewar bawa, babu iklasi a ibadarsa ga Allah kuma babu ihsani ga bayin Allah ” Duba Taisirul Karimir Rahman Fi Tafsiri Kalamil Mannani (1/19) bugun Almaktabatul Islamiyyati.

Ta’aliki :

Malam ya nuna mana abin da yake sadar da bawa ga rahamar Allah da nisantuwa daga ukubarsa da Azabarsa, shi ne bawa ya zama mai Ikhlasi a cikin ibadarsa, domin ibadar da babu iklasi a cikinta tamkar rubutu ne a kan ruwa.

Iklasi shi ne; tsantsanta bauta ga Allah shi kadai, ba tare da sanya kowa ba sai Allah. Watau bawa ya nufaci Allah da Aiyukansa. Yardar Allah yake nema a cikin ibadarsa gaba daya ba waninsa ba.

Babban Malami Abul Kasim Alkushairi Allah ya yi masa rahama ya ce:” Iklasi shi ne: dayanta Allah mai Tsarki kuma madaukaki a duk wani kuduri na da’a, shi ne, ya nufaci neman kusancin Allah Madaukaki da aikin da’a banda gauraya bautar da waninsa ko Shirka. kamar yin aiki don wani bawa ko neman yabon mutane ko son begen bayin Allah ko wani abu na da bam ba neman kusancin Allah ba.” Duba Hilyatul Abrari Wa Shi’arul Akyari Fi Talkisid Da’awati Wal Azkari Almustahabbati Fil Laili Wannahari shafi na 34, na Imam Annawawi, bugun Darubni Kasir.

Duk ibadar da babu iklasi a cikin ta, to babu ruwan Allah da ita. Allah ya ce :” Lalle Mu mun saukar da littafi zuwa gare ka da gaskiya, ka bauta wa Allah kana mai tsantsanta bauta a gare Shi.

* Ku saurari! Tatacciyar ibada ta Allah ce… ” Suratuz Zumar aya ta (2-3). Allah ya ce :” Duk wanda ya kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa, to ya aikata aiki na kwarai kuma kada ya sanya wani a cikin bautar Ubangijinsa ” Suratul Kahfi aya ta (110).

Allah ya labarta mana a cikin Alkur’ani mai girma; da a ce Annabawa za su yi Shirka a cikin bautarsa, to da ya rushe Aiyukansu.

Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya bayyana mana cewa :” Allah ya ce ; Ni na fi wadatuwa daga abokan tarayya duk wanda ya aikata wani aiki kuma ya yi tarayya da wanina a ciki, zan bar shi da Shirkarsa ” Muslim ne ya ruwaito a Sahihinsa.

Ihsani ga bayin Allah: yana nuna nagarta ta mutum da kuma kyakkyawar mu’amalarsa. Allah ya yi umurni da kyautata wa bayinsa a cikin Alkur’ani a wurare da dama kuma ya bayyana yana son masu kyautata wa. Allah ya ce :” Kuma ku kyautata, lalle Allah ya na son masu kyautawa ” Suratul Bakara aya (195). Allah ya ce :” Kuma ka yi hakuri, lalle Allah ba ya tozartar da ladan masu kyautatawa ” Suratu Hud aya ta (115). Allah ya ce :” Lalle rahamar Allah kusa take ga masu kyautatawa ” Suratul A’arafi aya (56).

Kyautatawa ta kunshi sada zumuci da taimakon Mabukaci da gina Makaratun Addinin dana Boko da Taimakon Makarantu da kayan aiki da gina Masallatai da taimakon dalibai da Malamai akan duk wani abu da zai bunkasa harkar koyo da koyarwar da daukar rayuwar Marayu da Nakasassu musamman ilmantar da su da duk wani abu kyakkyawa da idan aka yi zai faranta rai, yana shiga cikin ihsani.

Manzon rahama sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce :”Mafi alherin ku, wanda ya fi anfanar da mutane ” Imam Ahmad ne ya ruwaito a Musnad kuma Al-albani ya inganta shi a cikin Assahiha.

Allah ya tabbatar da mu akan tafarkin daidai. Amin.

Ustaz Nuhu Ubale Ibrahim
(Abu Abdilhalim)
Laraba:16th Safar, 1438 – 16/11/2016.

The post ALFAWA’ID NA (ABUBUWAN DA ZAMU FA’IDANTU DA SU) KASHI NA UKU appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>