Sanata Saidu Muhammad Dansadau Tsohon Sanata ne na yankin Zamfara Ta Tsakiya daga shekarar 1999-2007. Ya dade yana gwagwar maya domin ganin an samu ci gaban tsaro a Jahar Zamfara.
Idan bamu manta ba kwanakin baya ya rubutawa Shugaba Muhammad Buhari Budaddiyar wasika inda yayi kira da a saka Dokar ta Bace a Jahar Zamfara Domin Inganta tsaro. Inda ya bayyana cewa Gwamnan Jahar baya zama kuma bai damu da halin da talakawan sa suke ciki ba.
A yanzu haka Sanata Dansadau ya Shiga Kungiyar yan banga na Jahar wanda aka fi sani da Yan Sakai Domin basu karfin Guiwar yakan ta’addanci dake damun Jahar.
Ko menene ra’ayin dan gane da wannan abu da Sanata Dansadau yayi.
The post SANATA DANSADAU YA SHIGA KUNGIYAR YAN BANGA DOMIN TAIMAKAWA HARKAN TSARO A ZAMFARA appeared first on MUJALLARMU.