Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

DAUSAYI MAI NI’IMA TARIHIN ANNABIN RAHAMA (5)

$
0
0

Karnin Da Manzon Allah (SAW) Ya Rayu :

Fiyayen halitta Annabin Rahama Sallallahu Alaihi wa alihi wa sallam ya fi kowa kamala ta kowace fuska, ya fi kowa matsayi da daraja da martaba a wajen Allah, shi ya fi kowa kyakkyawar dabi’a a bayan kasa, shi ne wanda ya fi kowa dace wa da abokai, shi ne mafi kyawun halitta. Allah ya fifita karninsa akan KARNIN MUTANEN DUNIYA BAKI DAYA, karninsa cike yake da kyakkyawar zamantakewar rayuwa, ya zo da daidaito da adalci, karninsa cike yake da nagarta da alherai, duniya bata ga karnin da ya kai nasa ba tsawon tarihin duniya, ya samu duniya a cikin bakin duhu na zaluncin Shirka da Sabo, da Ta’addanci da… amma saboda alherin wannan BABBAN BAWAN ALLAH KUMA MANZONSA, sai ya kawo gyaran da ba a taba gani ba. Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce :” An aiko ni a cikin mafi alherin karnin bil adama, karni bayan karni har na kasance a cikin karnin da nake ciki ” Bukari ne ya ruwaito a cikin Sahihinsa (3557).

An karbo hadisi daga Sahabi Imrana dan Husain, Allah ya kara yarda a gare shi, Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce :” Mafi alherinku karni na, sa’an nan wanda yake biye mi shi, sa’an nan wanda suke biye da su ” Bukari ne ya ruwaito a Sahihinsa (2651) da Muslim a Sahihinsa (2535). A wata ruwaya ta Muslim da Abu Dawud a Sunan (4657),da Tirmizi a Aljami’u (2222) ce wa ya yi :” Mafi alherin wannan al’umma karnin da aka aiko ni a cikin su, sa’an nan wanda suke biye musu ”

Mutanen da suka kasance a tare da shi (wato sahabbai) su ne mafiya alherin mutane a wajen Allah, idan aka debe tawagar Annabawa da Manzanni, domin al’ummar Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ta fi kowace al’umma kamar yadda Allah ya labarta mana a cikin LittafinSa mai Tsarki. An karbo hadisi daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi, ya ce :annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce :” Mafi alherin alummata su ne wadanda aka aiko ni a cikinsu ” Muslim ne ya ruwaito a Sahihinsa (2534). Imam Annawawi ya ce :” Malamai sun hadu (ittifaki) akan mafi alherin karni gaba daya, karnin annabi Muhammad sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, kuma abin da ake nufi da karni sahabbansa ” dubu Alminhaj Sharhu Sahihi Muslim (16/89), na Imam Annawawi, bugun Almaktabatus Sakafi. Hafiz Ibnu Hajar shi ma ya tabbatar da haka a Fathul Bari.

Manzon rahama sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya bayyana mana al’umma ba zata gushe a cikin alheri ba, matukar akwai sahabbansa a cikin al’umma, inda ya ce :” Ba zaku gushe cikin alheri ba, matukar a cikinku akwai wanda ya ganni, kuma ya yi abota da ni (wato ya yi imani da shi), na rantse da Allah, ba zaku gushe cikin alheri ba, matukar a cikinku akwai wanda ya ga wanda ya ganni kuma ya yi abota da ni ” Ibnu Abi Shaiba ne ya ruwaito a Almusannaf, kamar yadda Alhafiz Ibnu Hajar ya bayyana a cikin Fathul Bari (7/274) bugun Darul Fikri.

Har-wa-yau Manzon tsira Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya labarta mana samun nasara a wajen ya ki matukar akwai sahabbai a cikin yakin. Ya ce :” Wani lokaci zai zo wa mutane, da za su yaki wasu jama’a, sai a ce da : shin a cikinku akwai wanda ya yi abota da Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam? Sai su ce da su : e, sai a yi musu budi (watau abasu nasara), sa’an nan wani lokaci zai zo wa mutane, da za su yaki wata jama’a, sai a ce da su: shin a cikin akwai wanda ya yi abota da wanda ya abota da Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam? Sai su ce: e, sai a yi musu budi, sa’an nan wani lokaci zai zo wa mutane da za su yaki wasu jama’a, sai a ce musu, a cikinku akwai wanda ya abota da wanda ya yi abota da wanda ya abota da Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam? Sai su ce :e, sai a yi musu budi ” Bukari ne ya ruwaito a Sahihinsa (3649), da Muslim a Sahihinsa (2532)
Imam Annabawa Allah ya yi masa rahama ya ce :” A cikin wannan hadisi akwai mu’ujizozin Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, da falalar sahabbai, da tabi’ai ” Duba Alminhaj Sharhu Muslim (16/89)
A ganina, Allah shi ne mafi Masani ; al’umma zata samu alheri matukar ta bi tafarkin wadannan nagartattun bayi, kuma zata gamu da tsiya, da tambada, da tabewa matukar ta ci zarafin wannan ayari mai albarka.

An tambayi Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam wadanne mutane ne mafi alheri? Ya ce : “Karnin da nake a cikinsa, sa’an nan na biyu, sa’an nan na uku ” Muslim ne ya ruwaito a Sahihinsa (2636). Abdullahi dan Mas’ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :” Lalle Allah ya yi tsinkaye cikin zukatan bayi, sai ya ga zuciyar annabi Muhammad sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ita ce ta fi alherin zukata, sai ya zabe shi, kuma ya aiko shi da manzancinSa, sa’an nan ya yi tsinkaye ka zukatan bayi bayan annabi Muhammad sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, sai ya samu zukatan sahabbansa su suka fi tsarki a cikin zukatan bayi, sai ya zabe su suka zamanto waziran annabinSa, suna yaki domin tsare addininSa ” Duba Alisti’aab Fi Marifatil Ashaab (1/13) Na Ibnu Abdilbar.

Abin mamaki duk da wadannan falalar da wannan karni da martaba, da alherai da yake da ita, to, a wajen shi’a ba haka yake ba, su a wajensu karni ne na azzalumai maciya amana inbanda tsiraru a cikinsu. Allah ya tsare mu da tabewa. Amin.

Mu hadu a rubutu na gaba, inda za mu tattauna akan garin Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam.

Ustaz Nuhu Ubale Ibrahim
(Abu Abdilhalim)
Litinin: 21st Safar, 1438 = 21/11/2016.

The post DAUSAYI MAI NI’IMA TARIHIN ANNABIN RAHAMA (5) appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>