Barayin shanu sun kashe a kalla mutane 9 a wani hari da suka kai yau a Jahar Zamfara.
Dan majalisa mai wakiltar Zurmi ta Yamma Yusuf Moriki ya tabbatar da wannan harin in da ya bayyana cewa abun ya faru ne a Kauyukan Dole, Tudun Bugaje da Kwangami dake karamar hukumar Mulki ta Zurmi.
A kwanakin nan da suka gabata Barayin shanun sun kai hare hare da dama wanda yayi sanadiyar tashin hankalin mutanen Jahar musamman na yakin da abun ya shafa.
Jama’a da dama suna kira da Gwamnatin tarayya da ta kawo agaji kamin Jahar ta Zamfara ta zama kamar Borno inda yan boko haram suka hana alummah walwala.
Allah kawo mana karshen wannan ta’adanci
The post INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN appeared first on MUJALLARMU.