Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

TUNATARWA: ALFAWA’ID NA 4

$
0
0

 

Al-imam Almawaradi Allah ya yi masa rahama ya
ce:”Karya ita ce ta tattara dukkan sharri, kuma ita
ce asalin kowane abun zargi, saboda munin
karshenta, da dattin nasararta, domin tana haifar
da annamimanci, shi kuma annamimanci yana
haifar da kiyayya, ita kuma kiyayya tana komawa
gaba, kuma atattare da adawa babu aminci, da
hutu a tsakanin al’umma. Don haka ne ake ce wa:
duk wanda gaskiyarsa ta yi karanci, to, abokansa
za su karanta. Gaskiya da karya suna shiga cikin
labarun da ya shude ( wato cikin tarihi), kamar
yadda cika alkawari da saba shi yake shiga cikin
al’amuran da za su zo. Gaskiya ita ce:bayar da
labari akan abu yadda yake(wato ba tare da ragi,
ko kari ba) , karya kuma ita ce:bayar da labarin
Abu ba a yadda yake ba( ta hanyar kara masa
gishiri) ” duba littafin Adabud Dunya Wad Dini
shafi na 295, na Al-imam Almawaradi, bugun
madabar Asariyya dake Lebanon, bugun farko na
shekarar 1427 bayan hijra.
TA’ALIKI:
1-Tabbas karya ita ce matattarar sharri gaba daya,
domin tana dora mai yin ta akan duk wani
gwadabe na fajirci. Manzon Allah (saw) ya ce:”
Lalle karya tana shiryarwa zuwa ga fajirci, kuma
lalle fajirci yana shiryarwa zuwa wuta, kuma lalle
mutum ba zai gushe ba yana karya kuma yana
kirdadon karya har a rubuta shi makaryaci a wajen
Allah ” Bukari da Muslim ne suka ruwaito. Allah ya
ce: “Kuma lalle fajirai tabbas suna cikin jahim”
Suratul Infidari aya ta 14. Manzon Allah (saw) ya
ce:”Alamar munafuki uku ne: idan zai magana ya
yi karya, idan kuma ya yi alkawari ya saba, idan
kuma aka ba shi amana sai ya cinye ” Bukari da
Muslim ne suka ruwaito. Don haka karya muninta
yana da yawa shi ya sa Al-imam Algazzali Allah
ya yi masa rahama ya ce: ” Karya tana daga cikin
munanan zunubai… ” duba Fathul Bari Sharhu
Sahihil Bukari (12/107) na Ibnu Hajar, bugun
madaba’ar darul fikri, bugu na daya na shekarar
1428 bayan hijra.
2-Annamimanci shi ne daukar maganar wani, ko
wasu zuwa ga wani, ko wasu domin bata
tsakaninsu. Wannan mummunar dabi’a tana hana
mai yin ta shiga aljanna. Manzon Allah (saw) ya
ce: “Annamimi ba zai shiga aljanna ba” Bukari da
Muslim ne suka ruwaito. Allah ya ce: “Tsakanin
azaba ya tabbata ga mai nuni da zunde” Suratul
Humazati aya ta 1. Allah ya ce:”Kada ka bi dukkan
wani mai yawan rantsuwa wulakantacce* mai
zunde mai yawo da annamimanci ” Suratul Kalami
aya ta 10-11. Manzon Allah ( saw) ya ce: ” Zaka
samu daga cikin mafiya iskancin mutane mai
fuska biyu, wanda zai je wa wadannan mutane da
wata fuska, wadannan da wata fuska ” Bukari da
Muslim ne suka ruwaito. Imam Annawawi Allah ya
yi masa rahama ya ce:”Sababin da ya sa aka
ce”daga cikin mafiya iskancin mutane ” Abu ne a
fili karara, domin tsantsar munafunci ne da
yaudara, da karya… ” duba Alminhàju Sharhu
Sahihi Muslimibnil Hajjàj (16/82) na Imam
Annawawi, bugun madaba’ar Sakafi dake Masar,
bugun farko na shekarar 2001 miladiyya. Abul
Abbas Alkurdubi Allah ya yi masa rahama ya ce: ”
Mai fuska biyu ya zamanto mafi sharrin mutane
domin halinsa hali ne na munafukai, saboda shi ya
saba da barna, da karya, mai shigar da barna a
tsakanin mutane. ” duba Fathul Bari (12/75).
3-Kiyayya da gaba da juna Allah ya hana muminai
yin ta, domin su ‘yan-uwan juna ne. Allah ya ce:”
Kadai muminai yan’uwan juna ne, saboda haka Ku
yi sulhu a tsakanin ‘yan’uwanku guda biyu (wato
idan sun samu sabani) kuma Ku ji tsoron domin ku
samu rahama ” Suratul Hujràti aya ta 10. Manzon
Allah ( saw) ya ce Musulmi dan’uwan musulmi ne
” Bukari da Muslim ne suka ruwaito. Manzon Allah
(saw) ya ce:”Baza ku shiga aljanna ba har sai kun
yi imani, kuma baza ku yi imani ba har sai kun so
junanku, shin bana nuna muku abin da idan kuka
aikata shi za ku so junanku ba? ku yada sallama a
tsakaninku ” Muslim ne ya ruwaito. Manzon Allah
(saw) ya ce: “Mumini da Mumini kamar gini ne,
sashinsa yana karfafar sashe” Bukari da Muslim
ne suka ruwaito.
4-Kasancewar karya da gaskiya na samuwa wajen
bayar da labari, da kuma wajen yada shi, sai ya
zamanto addinin Islama ba ya son yada jita-jita, da
abun da ba a da tabbacinsa. Allah ya ce: ” Kuma
Kada ka bi abin da baka da ilimi akansa, lalle ji, da
gani, da zuciya dukkaninsu abin tambaya ne ga
mutum ” Suratul Isra’i aya ta 36. Babban Malami
Katadatu Allah ya yi masa rahama ya ce:” Kada
ka ce ka gani alhalin baka gani ba, ko ka ji alhalin
baka ji ba, domin tabbas Allah Madaukaki mai
tambayarka ne akansu gaba daya ” duba Tafsirul
Kur’anil Azim (5/47) na Ibnu Kasir, bugun
madaba’ar Safa dake Masar bugun farko na
shekarar 1425 bayan hijra. Manzon Allah (saw) ya
ce:” Allah yana kyamatar muku abu uku: an ce
kaza, an ce kaza, da kuma yawan roko, da kuma
almubazzaranci da dukiya ” Muslim da Ibnu
Hibbàn ne suka ruwaito. Manzon Allah (saw) ya
ce: ” Ya ishi mutum karya ya bayar da labarin duk
abin da ya ji ” Hadisi ne tabbatacce Muslim ya
ruwaito shi a Mukaddimar Sahihinsa, da Abu
Dawud a Sunan. Imam Malik Allah ya yi masa
rahama ya ce: “Mutum ba zai kubuta daga karya
ba, matukar yana bayar da duk labarin da ya ji”
Mukaddimar Sahihu Muslim. Abdullahi dan Mas’ud
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: ” Ya ishi
mutum karya ya bayar da labarin duk da ya ji ”
Mukaddimar Sahihu Muslim. Allah Shi ne mafi
sani.
Mu hadu a rubutu na gaba
Dan’uwanku a Muslunci
Abu Abdilhalim Nuhu Ubale Ibrahim.

The post TUNATARWA: ALFAWA’ID NA 4 appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>