Wani yaro ne dan masu hannu da shuni mai suna
Nazeeru, ya tashi cikin wadata da kwanciyar
hankali, amma baya samun kudi ko kadan
agurin mahaifansa, wannan abu yana bashi haushi.
Wata rana yana tare da abokinsa Nazeefi sai yake masa korafi akan abinda yake damunsa, sai abokinsa yake bashi shawarar idan har yana son samun kudi to kawai yadinga cewa ‘munsan komai fa kawai shiru muke’.
Shike nan kuwa, sai Nazeeru ya tafi gida yana zuwa ya tarar da momynsa, kawai sai yace mata ”munsan komai fa momy, kawai shiru muke”. Sai momy dinsa tace ‘kai !, yi shiru d’an nan, zo nan kar6i wannan’, kawai ta
bashi Naira dubu biyar #5000, ai kuwa Nazeeru sai yace aw abin hakane, bara shima Dady na yazo, kawai sai yazo gate ya tsaya, Dadynsa na zuwa yace, ”Dad munsan
komai fa, shiru kawai mukeyi”
Kawai sai Dad dinsa yace, kai ! Nazeeru yi shiru kada ka bari mominka taji, kawai ya dauko Naira dubu goma #10,000 ya bashi.
Nazeeru kuwa yace lalle abin nema yasamu kamfani yabude, sai kawai ya tafi gurin
maigadin gidan su yace ”Baba wallahi munsan
komai, shiru kawai mukeyi”.
Kawai sai maigadin ya rungume shi yace ‘Nagodewa Allah daka gane nine na haifeka……
Idan kaine ya zakayi ???
Because Kaima Me Karantawa Munsan Komai Paaaa …
The post MUSHA DARIYA: MUN SAN KOMAI FA, KAWAI SHIRU MUKE appeared first on MUJALLARMU.