1. Sujjada Qabli ana yinta ne
kafin sallama. Bayan mutum
yayi tahiya, kafin yayi sallama, sai ya sake yin wasu sujjadu
guda biyu, sannan ya sake yin
wata tahiyar, Sannan yayi
sallama. Wannan ita ce Sujjada
Qabaliy, Dalilan da suke sawa
ayi ta: Idan mutum yayi ragi a cikin Sallarsa, Ko kuma ya
tauye wasu sunnoni Qarfafa
guda biyu ko sama da haka. (a takaice kenan).
2. SUJJADA BA’ADI: ana yinta ne
duk yayi da aka Qara wani abu acikin Sallah. Ko kuma yayin da
mutum ya mance da wata
farillah, ko kuma rukuni daga
cikin sallar sa. Bayan ya kawo
wannan farillar da ya mance, to
sai yayi sujjada Ba’adi.
YADDA AKE YINTA: Ana yinta ne
bayan anyi tahiya anyi sallama,
sai a sake yin wasu sujjadu
guda biyu, sannan ayi tahiya ayi sallama.
ALLAH YASA MUDACE
The post MUKOYI IBADA: SUJADAR QABLI DA BA’ADI appeared first on MUJALLARMU.