Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Muhd Bashir Amin: ⁠⁠⁠DAUSAYI MAI NI’IMA TARIHIN ANNABIN RAHAMA NA 6

$
0
0

Allah madauki ya tayar da annabinSa sallallahu alaihi wa alihi wa sallam a garin makka. Wannan gari na Makka, gari ne mai tarin albarka, da falala, gari ne na aminci da alherai masu din bin yawa, gari ne da duk wani mutumin kirki yake sonsa, da shaukin ziyartar sa, kuma ya samo wannan falala da daraja ne ta sanadiyyar annabi Ibrahim sallallahu alaihi wa alihi wa sallam. Inda ya roki Allah, ya ce :” Kuma ka anbaci lokacin da Ibrahim ya ce : Ya Allah! Ka sanya wannan gari ya zama amintacce, kuma ka azurta mutanensa da ‘ya’ yan itatuwa wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira daga cikinsu, sai Allah ya ce wanda ya kafirta ma zan jiyar da shi dadi kadan, sa’an nan kuma na tilasta masa shiga wuta, kuma makomarsa ta munana *…Ya Allah ka aiko da wani Manzo daga cikinsu, yana karantar da su Alkur’ani da Hadisi, kuma yana tarbiyyantar da su, kuma lalle kai ne Mabuwayi Garabadau ” Suratul Bakara aya ta (126-129).

Garin maka gari ne madaukaki, daga cikin abin da zai nuna daukakarsa shi ne ; yawan sunayen da ake kiransa da su, domin yawan suna yana nuni da bayyanar da daukakar abu da matsayinsa da dajarsa, Daga cikin falalar wannan gari da babu wani gari da ya same ta ita ce ; kasancewar garin fiyayyen halitta ne, wanda babu mai matsayi da daraja da martaba a wajen Allah da ya kai shi, kuma gari ne na badadayin Allah annabi Ibrahim (watau Kalilullahi) sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, kuma gari ne na annabi Isma’il sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, kuma gari ne na dakin Allah, inda dukan musulmin duniya suke haduwa domin sauke daya daga cikin rukunan Muslunci watau aikin Hajji, kuma kuma nan alkibilar musulmi take, wanda duk bai fuskance ta ba da gangan, to, bashi da salla. Gari ne da duk mumini yake sonsa, kuma yake fata da kwadayin zuwansa, wuya da wahala bata sa musulmi ya daina sonsa, babu wani WAJE da musulmi yake shaukin zuwa kamar wannan gari badon komai ba sai don matsayi da girma da kima da martaba da kwarjini da Allah ya yi wa wannan gari, tare da kebance shi da wasu hukunce-hukunce. Makka gari ne na ni’ima, duk da asalisa kekashasshen gari ne amma Allah ya zuba masa tarin albarka, da dinbin alherai sanadiyyar addu’a da annabi Ibrahim sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya yi.
Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya bayyana garin Makka a matsayin gurin da ya fi alheri a doron kasa, kuma Allah ya fi so, inda :”Na rantse da Allah, lalle ke ce (Makka) mafi alherin Kasar Allah, mafi soyuwar kasar Allah a wajen Allah, ba don an fitar da ni ba daga cikin ki, da ban fita ba” Hadisi ne ingantacce Tirmizi ne ya ruwaito a Aljami’u (3934),da Ibnu Maja a Sunan (3108).

Tanbihi : Akwai wani hadisi da Imam Addabarani ya ruwaito, wai annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce :”Madina ta fi Makka alheri ” to wannan hadisi ne munkari, mai rauni kwarai, bai inganta ba kamar yadda Imam Azzahbi Allah ya yi masa rahama ya bayyana. Domin ganin haka duba Tuhfatul Ahwazi (9/385) Na Mubarak Furi, bugun Darul Hadis.
Sunayen garin Makka ; wannan gari mai albarka yana da sunaye masu yawa da Alkur’ani ya ammbata, ga wasu daga cikin su… Mu hadu a rubutu na gaba.

Allah ka kara mana son wannan gari a zukatanmu da gabbanmu da aiyukanmu. Amin.

Nuhu Ubale Ibrahim
(Abu Abdilhalim)
28th Safar, 1438.

The post Muhd Bashir Amin: ⁠⁠⁠DAUSAYI MAI NI’IMA TARIHIN ANNABIN RAHAMA NA 6 appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>