Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Za’a Haramta Sayar Da Shinkafa ‘Yar Gwamnati a Wata Jaha a Nijeriya

$
0
0

Gwamnatin Nijeriya dai dama ta dade ta na yunkurin dakile shigowar shinkafar turai wacce ake kira shinkafa ‘yar gwamnati domin ta bunkasa noman shinkafa ta gida da kuma dogaro da kai.

Toh sai gashi gwamnan jahar Ebonyi ya bayyanan nufin sa na jaddada wannan manufa a jahar sa.

Gwamnan Mr Dave Umuahi ya fadawa wata tawagar hafsosin soja wanda suka kai masa ziyara cewa zai jagoranci wata runduna da ta kunshi manya jami’an gwamnati wanda aikinsu kawai shi ne su hana saya da sayarwar shinkafar gwamnati a kasuwanni a fadin jahar.

Ya ce dalili shi ne domin ya kara karfafa kudirin gwamnati na samun dogaro da kai a bangaren samar da abinci a fadin kasar. Ya kara da cewa gwamnatinsa na goyon bayan gwamnatin tarayya game da rage shigowar shinkafar da ake yi kasar.

Duba da yadda jahar ta Ebonyi ta kasance daya daga cikin jahohin da suka fi noman shinkafa a Nijeriya, gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar hakan.

Ya kara da cewa da yawa daga cikin shinkafar da ake shigowa da ita kasar ba mai kyau ba ce, wannan ya sa ta kan lalacewa cikin watanni shida kacal, kuma duk da haka a ci gaba da sayar da su.

Ya ce yana da muhimmanci ‘yan Nijeriya su mayarda hankulansu wajen cin shinkafar gida domin kuwa ta fi lafiya.

daga alummata.com

The post Za’a Haramta Sayar Da Shinkafa ‘Yar Gwamnati a Wata Jaha a Nijeriya appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050