Gwamnatocin Nigeria da Kamaru sun ce akwaibuƙatar kafa wata kotu ta musamman da za a gurfanar da dubban mutanen da aka kama a ƙasashen biyu bisa tuhumar zama ‘yan ƙungiyarBoko Haram.
Wannan dai na ƙunshe a cikin sanarwar bayan taron da aka fitar a ƙarshen ziyarar da shugaba Paul Biya ya kawo Najeriya.
Kungiyar Boko Haram na matsa kai hare-hare a kasashen biyu. Najeriya da Kamaru sun kuma sanya hannu kan yarjeniyoyi daban-daban da suka shafi tattalin arziƙi da zamantakewa.
The post ZA A KAFA KOTU KAN YAN BOKO HARAM appeared first on MUJALLARMU.