ANA SARAN BUHARI ZAI SA HANNU A KASAFIN KUDIN BANA YAU
A yau ne ake saran Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu a kasafin kudin bana,Rahotanni daga Jaridun Safiyar yau sun bayyana hakan.
Bayan wannan tsawon Lokacin ana jiran Kasafin kudin bana domin komai ya tsaya a kasar nan saboda kudi basu yawo, Rahotanni na bayyana cewa Yan Majalisa sun maidawa shugaba Buhari kasafin kudin a jiya, inda ake saran zai sa masa Hannu ayau.
An shaidawa Yan jarida cewa yanzu haka yan majalisun sun maida kasafin kudin bana kamar yadda shugaba Buhari ya kai musu shi. kuma ana saran Shuagab Buhari zai gasgata hakan kuma yasa hannun ayau.
The post LABARI DA DUMI DUMIN SA AKAN KASAFIN KUDIN BANA appeared first on MUJALLARMU.