Ana zargin mahara kan yi amfani da hijabin wajen boye bama-bamai a hare-haren da suke kai wa, wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a shiyyar arewa-maso-gabashin kasar.
Yayin da wasu ke goyon bayan haramta sanya hijabin, wasu kuma na adawa da hakan, suna cewa sutura ce da addinin musulunci ya tanadar, don haka ya kamata jami’an tsaro su tsaurara bincike, maimakon haramta hijabi.’Yan magana dai kan ce ɗan kuka shi ke ja wa uwa jifa! Yayin da al’ummar musulmi a Najeriya ke alfahari da suturar mata ta hijabi da lullubin himar, sakamakon yadda yake rufe tsiraici da kare martabar mata, babban kalubalen da wannan sutura ke fuskanta shi ne zargin da ake yi cewa mayakan boko haram na amfani da ita wajen kai harin kunar-bakin-wake, musamman a shiyyar arewa masu gabashin Najeriya, inda rikicin boko haram din ya fi kamari.
Duk da irin ikirarin da jami’an tsaro ke yi na karya-lagon kungiyar Boko Haram, bincike na nuna cewa idan da wani abin da ke tsole-idon jami’an tsaro da kuma al’umomin da ke yankunan da ke fama da irin wannan harin kunar-bakin-wake a halin da ake ciki, babu kamar bad-da-sawun da maharan ke yi ta hanyar amfani da hijabi.
Wani jami’in kato-da-gora, wato matasan da ke tallafa wa jami’an tsaro a jihar Borno da ya nemi a a sakaya sunansa ya ce, “Muna sa ido sosai a kan maza da mata, sai dai yawanci masu kawo harin su kan saka himar ne wadatacce kuma mai kyau wanda da wuya ka gane su.”
The post ME NENE RA’AYIN KU KAN HANA SA HIJJABI A NAJERIYA appeared first on MUJALLARMU.