Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

BAI KAMATA YAN SIYASA SU RINKA AMFANI DA AL’QURNI DA BILBLE WAJEN RANTSUWA BA

$
0
0

GWAMNAN JIHAR IMO ROCHAS YACE BA DAI DAI BANE YAN SIYASA SU RINKA AMFANI DA LITTAFAI MASU TSARKI WAJEN RANTSUWA.

Rahoton dake zuwa muna daga gidan Talabijin maisuna Liberty Tv dake kudancin Nijeriya ya Bayyana cewa Gmamnan Jihar Imo Dr Rochars Okoracha yace bai kamata ace ‘Yan siyasar kasar nan suna amfani da littafai masu tsarki wajen rantsuwa ba.

Rochas yace dai amfani da littafan biyu Al’qurni da Bilble kuskure ne,saboda littafai ne da sukeda tsarki dan haka bai kamata arinka amfani dasu ba.

Gwamnan yayi wannan bayani ne a inda ya halacci wani taro na cibiyar wayar kai da kungiyar al’adun gargajiya ta shirya na musamman.

Gwamna Rochas Okoracha ya bayyana abubuwan daya kamata ace yan siyasar kasar na amfani dasu wajen rantsuwa kamar haka:-

1-Yan arewa musulmai kenan su rinka rantsuwa da (Kwarankwatsa)

2_Yarbawa kuma su rinka rantsuwa da (Amadioha)

3-Inyamurai kuma su rinka rantsuwa da (Abubuwan su na bautar gargajiya)

Gwamnan ya kara da cewa wannna itace hanya da tafi dacewa ga yan siyasa amadadin amfani da littafai masu tsarki,domin littafai akwai Rahama acikin su.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

The post BAI KAMATA YAN SIYASA SU RINKA AMFANI DA AL’QURNI DA BILBLE WAJEN RANTSUWA BA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050