Rahotanni na nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida Nijeriya a gobe Juma’a, 10 ga watan Maris, inda Allah ya kai mu.
Wannan bayani ya fito ne a wata sanarwa da mataimakin shugaban kasan na musamman a kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya wallafa a shafin sa na Facebook.
Shugaba Buhari ya bar gida Nijeriya a ranar 19 ga watan Janairun shekarar nan zuwa birnin London inda ya je hutu, tare da duba lafiyar sa.
Shugaba Muhammad Buhari yayi godiya ta musamman ga dumbin ‘yan Nijeriya da suka yi ta yi masa addu’o’i yayin da yake fama da rashin lafiya.
The post OYOYO SHUGABA MUHAMMAD BUHARI ZAI DAWO GIDA NIJERIYA GOBE JUMA’A-INJI FEMI ADESINA appeared first on MUJALLARMU.