Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

LABARI CIKIN HOTUNA SOJOJIN NIJERIYA SUNYI NASARAR KAMA MUTUMIN DA KEYIWA YAN BOKO HARAM LEKEN ASIRI

$
0
0

A yau ne rundunar sojan Nijeriya tayi nasarar cafke wani dan leken asirin yan boko haram a wani kauye dake Borno.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri, Alhassan Garba

Kaakakin watsa labarai na rundunar sojan kasa Birgediya Sani Kukasheka Usman ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 9 ga watan Maris inda yace:“Dakarun runduna ta 232 sun gudanar da sintiri a kauyukan Muchalla, Lade da Bodeno sun don tabbatar da yayan Boko Haram basu sake komawa kauyukan ba. Haka zalika sun gudanar da wani sintirin a kauyen Garkida har zuwa Dzangwalla inda suka hallaka wasu yan Boko Haram da suka tsere daga dajin Sambisa.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

Usman yace dakarun sojan runduna ta 27 kasa sun cafke Alhassan Garba, mutumin dake tattara ma Boko Haram bayanan sirri, tare da yi musu leken asiri.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

Yace: “Bayan samun bayanan sirri daga wasu yan kishin kasa, Dakarun runduna ta 27 sun smau nasarar cafke mutumin dake tattara ma Boko Haram bayanan sirri, tare da yi musu liken asiri, mai suna Alhassan Garba a kauyen Azare dake karamar hukumar Gujba na jihar Yobe.

“Bincike ya nuna cewar diyar Alhassan, Lami ALhassan Garba na auren wani kasurgumin dan Boko Haram mai suna Musa Isah, wanda ya tsere daga kauyen zuwa jihar Kano, kuma min bi shi hark anon, mun kama shi, a yanzu dukkaninsu suna hannu ana gudanar da bincike akan su.”

Dan Boko Haram, surukin Alhassan Garba

Usman ya cigaba da fadin: “Dakarun runduna ta 233 tare da hadin gwiwar rundunar hadaka ta 29 da dakarun runduna ta 212 sun gudanar da aikin kakkabe yan ta’adda a kauyen Lawanti. Kazalika dakarun rundunar hadaka ta 154, da na 29 sun gudanar da sintiri cikin shirin ko-ta-kwana akan hanyar Mauli da Alagarno don mamaye yankin daga hana yan Boko Haram samun wurin buya.

“Dakarun sun sake yin wani sintiri akan hanyoyin kauyukan Sansan da Bulabulin shima don hana ma yan Boko Haram sakat. Suma dakarun rundunar hadaka ta 156 tana gudanar da nata sintirin a yankin Ngula-Jayiwa da Kukuram-Abalam don hana ma yan Boko Haram mabuya.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

“Suma runduna na 231 da 331 dake jibge a kudancin Borno ba’a barsu a baya ba, inda suke cikin shirin kota kwana sun gudanar da sintiri tare da kai samame a yankunan nasu.”

The post LABARI CIKIN HOTUNA SOJOJIN NIJERIYA SUNYI NASARAR KAMA MUTUMIN DA KEYIWA YAN BOKO HARAM LEKEN ASIRI appeared first on MUJALLARMU.

Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>