Majalisar dinkin duniya ta ce duniya na fuskantar babban bala’in yunwar da rabon ta da fuskantar irin sa tun shekarar 1945, tana mai roko a dauki matakan kauce masa.
Babban jami’in bayar da agaji na majalisar Stephen O’Brien ya ce fiye da mutum miliyan 20 ne ke fuskantar bala’in yunwa da fari a Yemen, Somalia, Sudan ta Kud da Nigeria.
Tuni dai hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, Unicef ta yi gargadin cewa yara 1.4m ka iya mutuwa sakamakon yunwa a wannan shekarar.
Mr O’Brien ya ce ana bukatar $4.4bn zuwa watan Yuli domin kauce wa wannan bala’i.
A cewar Mr O’Brien “Kananan yara sun tsimbire sannan ba sa zuwa makaranta. Rayuwarsu na cikin bala’i. Hakurin da jama’a ke yi na neman karewa. Mutane da dama za su rasa muhallansu sanna za su ci gaba da neman yadda za su rayu, lamarin da zai kawo tashin hankali a yankunan.”
The post DUNIYA NA FUSKANTAR MASIFA appeared first on MUJALLARMU.