Ranar Jama’ar data gabata ne aka sa ran bayyanar Jaruma Nafisa Abdullahi gaban Kotu ta 33 dake zamanta a Unguwar Dorayi dake Birnin Kano. An dai gurfanar da Jarumar ne bisa zargin daina halartar ɗaukar fim ɗin MUTUWAR AURE Wanda Kamfanin Almubarak International Fim Production ke ɗaukar nauyin shiryawa.
Ana zargin Jaruma Nafisa Abdullahi da daina ci gaba ɗaukar shirin fim ɗin, a cewar Jamilu Ahmad Yakasai shugabata Kamfanin Almubarak International Fim wanda shi ne Production, Nafisa Abdullahi ta daina
zuwa wurin ɗaukar shirin wanda anyi nisa da ɗaukar fim, yau sama da wata tara ke nan amma Nafisa Abdullahi ta daina zuwa ba tare da bayar da wani dalili ba. Hakan tasa aka gurfanar da ita gaban kotu mai lamba 33 dake Dorayi, amma ranar da aka shirya fara sauraran kara taki halartar zaman kotun, saboda haka yanzu ana shirin ɗaukar matakin da ya kamata inji Dakan Daka
The post AN GURFANAR DA NAFISA ABDULLAHI A KOTU wacce kuka sani da nafisa sai watarana appeared first on MUJALLARMU.