Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

WATA ME CIKI TA KAI HARI A BARNO

$
0
0

Jami’an tsaro a Maidugiri da ke jihar Bornon Najeriya sun kashe wata mata da tayi yunkurin kai harin kunan-bakin-wake a birnin.

  dan sandan jahar Victor Isuku ya fitar da cewa, “matar me kimanin shekara 18 ne ta yi yunkurin kunan-bakin-wake, amma ‘yan kato-da-gora sun gan ta sannan jami’an tsaro sun harbe ta har lahira”.

Ya kara da cewa matar ta so kutsa kai ne wani wuri ranar Asabar amma Allah bai ba ta sa’a ba.

Rahotanni sun ce matar na dauke da juna biyu ne.

Ishaku ya ce  babu wanda ya mutu ko jikkata, kodayake ma’aikatan agaji sun ce daya daga cikin ‘yan kato-da-gorar ya jikkat

Kungiyar Boko Haram dai na yin amfani da matar sosai wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake, inda a kwanakin baya suka fito da salon yin amfani da matar dauke da jarirai domin bad-da-sawu.

Hakan na faruwa bayan rundunar sojin kasar ta ce ta ci karfin su, lamarin da ya sa suka rasa mafaka.

Kiyasi ya nuna cewa rikicin kungiyar ta Boko Haram ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 20,000 sanna ya tilasta wa fiye da mutum 2.6m barin gidajensu.

The post WATA ME CIKI TA KAI HARI A BARNO appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>