Tsohon Gwamnan babban bankin CBN Farfesa Charles Soludo ya soki tsare-tsaren tattalin arziki na wannan Gwamnati. Soludo ya bayyana wannan ne a wani taro da aka yi domin gyara tattalin arzikin Najeriya.
Soludo ya soki tsarin tattalin arzikin Buhari
Farfesa Soludo yace Jam’iyyar Buhari ta zo da maradu da alkawura iri-iri kafin ta hau mulki sai dai yanzu babu wani abin a zo- a gani a kasa Inji Farfesan.
Soludo ke cewa har yanzu kudin da ake kashewa a albashi ya zarce abin da ake kashewa wajen ayyukan gina kasa. Farfesa Soludo yace babu wani abin da ya canza a wannan Gwamnati ai ikirarin canji.
Soludo ya soki tsarin tattalin arzikin Buhari
Idan ba a manta ba an yi ‘yar rigima da musayar kalamai tsakanin Adams Oshiomole tsohon Gwamnan Jihar Edo da kuma Farfesa Charles Soludo tsohon Gwamnan CBN na kasa. Soludo ya zargi Gwamnatin Buhari da jagwalwala tattalin arzikin Najeriyda inda Oshiomole ya maida masa da martani.
The post TSOHON GWAMNAN BABBAN BANKIN NIJERIYA YAYI TIR DA TSARE TSARE SHUGABA BUHARI AKAN TATTALIN ARZIKIN KASA appeared first on MUJALLARMU.