Hukumar sadarwa ta kasa NCC ta zabi jarumin finafinan Hausa Ali Nuhu a matsayin jakadanta a shirye-shiryen da ta ke yi na gudanar da bikin kaddamar da gangamin makon masu amfani da wayoyin sadarwa.
A wata sanarwa da Mista Tony Ojobo kakakin hukumar ya sa hannu ta ce, za a gudanar da bikin kaddamar da gangamin ne a ranar Laraba 15 ga watan Maris, wanda ya zo dai dai da ranar kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta duniya mai taken “samar da na`urorin da mai amfani zai aminta”
Babban batu a taron da za a gudanar a helkwatar hukumar NCC a Abuja shi ze, fito da dabi’un masu amfani da tarho a Najeriya.
An zabi wasu manyan masu nishadantarwa guda 2 ciki har da Ali Nuhu don su nuna yadda dabi’ar mai amfani da kayayyaki ta ke. A cewar sanarwa.
Mai masaukin baki a bikin, kuma shugaban hukumar NCC, Farfesa Umar G. Dambatta, a wani jawabi da yayi a lokacin ba Ali Nuhu jakadancin ya ce, kare hakkin masu amfani da tarho da samar da ‘yanci, su ne ginshikan manufofin shugabancinsa guda 8.
Kuma saboda haka ne hukumar ta sadaukar shekarar 2017 ga jin dadin masu amfani da wayar tarho wadanda suka hada da muhimman batutuwa a shekarar ta jin dadin masu amfani da wayar tarho wadanda suka hada da;
Wayar da kai game ingancin aiki, dandalin lantarki da mayen karfe (EMF), da Kar a dame ni (DND) wanda za a yi amfani da shi wajen tsayar da sakwannin ba gaira ba dalili da kuma kira kyauta zuwa hukumar a yayin da kamfanonin layin wayar salula su ka kasa yin wani abu game korafin jama’a.
Kamfe din na fatan samun goyon bayan masu kamfanonin wayar salula do cimma manufar samun ingancin aiki musamman katsewar kira.
Kwanannan hukumar ta samu labarin zanga-zangar rashin inganci musamman katsewar kira da rashin karfin sabis.
Shekarar ta kamfe din masu amfani da wayar salula za kuma ta gabatar da wani shiri mai taken “NCC Consumer Conservation” wanda hukumar ta shirya a duk yankunan kasar nan guda shida.
Ali Nuhu na daya da cikin fitattun jaruman finafinan Hausa da ke jan hankalin matasa a da kuma sauran jama’a da irin salonsu na nishadantawa.
The post JARUMIN FINA FINAN HAUSA ALI NUHU YA ZAMA JAKADAN NAJERIYA appeared first on MUJALLARMU.