Kasar Saudiyya Ta Haramtawa Wasu ‘Yan Kasar Qatar Aikin Hajji Da Umrah.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
A dalilin yanki hulda tsakanin kasar saudiyya da kasar Qatar ya jefa wasu ‘yan kasar dake zaune a kasar ta saudiyya da masu aikin hajji tsaka mai wuya.
A wani Rahoho da jaridar kasar Qatar ta fitar wani shugaban kwamitin kare hakkin dan adam Ali Ibn Sumaikh ya bayyana rashin jindadin sa game da yadda yan kasar ke fuskantar barazanar hana su aikin hajji da umrah.
Kwamitin yace a Rahoto da suka samu daga kasar Saudiya alamu na nuna cewa akallah sama da mutane 700 ne aka hana gudanar da aikin hajji da umrah acikin kwanaki 5.
Abaya dai munji cewa kasar ta Saudiyya ta haramta sa rigar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a kasar ta Saudiya mai dauki da sunan Kasar Qatar,wanda hakan yasu janyo kuce kuce a tsakanin kasashen biyu.
The post KARANTA KAJI: KASAR SAUDIYYA TA HARAMTAWA ‘YAN KASAR QATAR SAMA MUTUM 700 AIKIN HAJJI DA UMRAH appeared first on MUJALLARMU.