Kamfanonin sadarwa na MTN da Airtel sun gurfana gaban kwamitin majalisar wakilan Nijeriya domin amsa korafin dalilian da ya sa suke sallamar ma’aikatansu babu gyaira babu dalili
Wajen mayar da martani ga wannan tuhumar da aka yi wa kamfanonin biyu, jami’i mai kula da harkokin ma’aikata na kamfanin MTN, Ajibola Opeoluwa-Calebs yashaidawa shugaban kwamitin harkokin sadarwa na majalisar wakilan Nijeriya, Honarabul Saheed Fijabi cewa a cikin mutane 368 da suka bar aiki a MTN a shekarar da ta gabata, ma’aikata 174 suka kora saboda sun gaza cika sharuddan kamfanin na tafiya da zamani a kimiyyar sadarwa.
Ya ce “Harkar sadarwa harka ce da ke samun ci gaba a kodayaushe a kimiyyance, amma wadancan ma’aikata da suka fuskanci kora ba su da kwarewar da za su iya aiki da sabon fasahar da aikin nasu ya zo da shi”
“Ragowar ma’aikata 194 kuwa su suka bar aiki akan ra’ayinsu”, in ji jami’in na MTN
“Har wa yau, MTN ta samar da guraben aiki wa mutane 150 don su maye guraben wadanda suka bar aiki ko aka kora saboda rashin kwarewa”
Mista Caleb ya bayyanawa ‘yan majalisar cewa MTN na nan na yin wani shirin na daukar mutane 240 nan ba da dadewa ba
Shi ma a nasa bayanin, jami’in harkokin ma’aikata na Airtel, Gbemiga Owolabi ya bayyana wa kwamitin majalisa cewa, a cikin shekara daya da ta wuce mutane 90 ne kawai suka bar aiki a Airtel. Cikin 90 din, 66 su suka rubuta takardar barin aiki bisa ra’ayinsu na kashin kansu, an kori 6 saboda samunsu da laifuka daban-daban sa’annan kuma an kori ma’aikata 14 sakamakon rashin kwarewa da gamsar da kamfani cewa za su iya aiwatar da aikin da aka daukesu su aiwatar