Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all 3050 articles
Browse latest View live

KARANTA KAJI: GWAMNATIN TARAYYA NA KOKARIN GINA WA EL-ZAKZAKY SABON GIDA-(Lai Muhammad

$
0
0

Dalilin da ya sa El-Zakzaky ke a tsare har yanzu – Lai Mohammed.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Ibrahim El-Zakzaky na a tsare tare da iyalinsa da ma wasu manyan mabobi kusan sama da shekara daya bayan wani karo da hukumar sojin Najeriya Lai Mohammed, ministan bayanai da al’adu, ya ce baya tsare amma yana karkashin kulawa Ministan bayanai, Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da tsare shugaban kungiyar ‘yan shi’a Ibrahim El-Zakzaky ne saboda har yanzu bata sama masa gida ba.             
A cewar ministan, kotu ta bada umurnin sakin El-Zakzaky bayan an gina masa sabon gida. Ya yi bayanin cewa babu wani an kasar da zai amince da shi a matsayin makwabci, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta yanke hukunci ajiye shi a guri mai tsaro a Abuja.
Mohammed ya kara da cewa, shugaban kungiyar wanda hukumar soji ta kama a watan Disamba na shekarar 2015 baya gidan yari ko hannun hukumar DSS, A maimakon haka, ya ce El-Zakzaky na karkashin kulawa tare da iyalinsa, ya kara da cewa gwamnatin tarayya bazata iya kin bin umurnin kotu ba dangane da shugaban na kungiyar Shi’a da tsohon mai ba kasa shawara a harkan tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya).

The post KARANTA KAJI: GWAMNATIN TARAYYA NA KOKARIN GINA WA EL-ZAKZAKY SABON GIDA-(Lai Muhammad appeared first on MUJALLARMU.


BAYAN SABON AURE AN NADA AHMAD MUSA SARAUTA

$
0
0

Bayan auren sabuwar mata, an nada ma Ahmed Musa sarauta.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

An gudanar bikin ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2017 – Daliban arewacin Najeriya ne suka nada ma Musa sarautan Jagaban Matasan Arewa Kungiyar daliban arewacin Najeriya sun nada ma Dan wasan na kungiyar Super Eagles Ahmed Musa sarauta a matsayin Jagaban Matasan Arewa.
      
An yi bikin nadin sarautar Ahmed Musa wanda ya auri sabuwar amarya a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2017 a lokacin kaddamar da gurin wasansa a jihar Kano. Taron ya samu halartan manyan mutane ciki harda shugaban wasanni na jihar Kano, Ibrahim Galadima.
Ahmed Musa sarauta Mahaifiyar Musa da sauran ‘yan uwansa sun halarci taron a Kano a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, 2017. Kalli hotunan a kasa: Bayan auren sabuwar mata, an nada ma Ahmed Musa sarauta An nada ma Ahmed Musa sarauta Bayan auren sabuwar mata, an nada ma Ahmed Musa sarauta Bayan auren sabuwar mata, an nada ma Ahmed Musa sarauta

The post BAYAN SABON AURE AN NADA AHMAD MUSA SARAUTA appeared first on MUJALLARMU.

WATAN RAMADANA: KUNGIYAR KWANKWASIYYA AMANA TA RABA BUHUNAN SHINKAFA GA ‘YAN UWA MUSULMAI

$
0
0

Watan Ramadana: Kwankwaso yayi rabon shinkafa Watan Ramadana:

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kungiyar Kwankwasiyya tayi rabon kayan masarufi domin tallafa ma yayanta – Cikin abubuwan da aka rarraba har da shinkafa Kungiyar siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanata mai wakiltar al’ummar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa

                                          
 Kwankwaso, wato Kwankwasiyya tayi rabon kayan masarufi domin tallafa ma yayanta a watan Azumin Ramadana. Madugun Kwankwasiyya, Sanata Kwankwaso yaga dacewar taimaka ma mabiyansa a siyasa, har da sauran yan uwa musulmai a wannan wata mai alfarma domin dacewa da falalar dake tattare da hakan.
            
 A ranar Litinin 13 ga watan Yuni, jirgin alherin ya isa jihar Adamawa, inda kungiyar Kwankwasiyya ta mika ma takwararta mai suna Buhari-Osinbajo-Again (BOA) buhunan shinkafa domin raba ma jama’a.
Shinkafa Haka zalika a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni, Kwankwasiyya Amana ta aika da buhunan shinkafa guda dari 400 jihar Neja ta hannun kallabi tsakanin rawwuna Hajiya Amina HOD.
Dandalin Mujallarmu.com ta kalato cewar har yanzu sanata Kwankwaso bai hakura da kokarin neman taka takarar shugaban kasa ba.
Ga sauran hotunan: Watan Ramadana: Kwankwaso yayi rabon shinkafa Shinkafa

The post WATAN RAMADANA: KUNGIYAR KWANKWASIYYA AMANA TA RABA BUHUNAN SHINKAFA GA ‘YAN UWA MUSULMAI appeared first on MUJALLARMU.

DANDALIN KANNYWOOD: KARANTA KAJI ABINDA SANI DANJA YACE GAME DA RASHIN WAYEWAR ‘YAN FIM

$
0
0

Dandalin Kannywood: Akwai rashin wayewa sosai a tsakanin yan fim – Sani Danja.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Jarumi Kuma Mawaki Sani Danja yace akwai rashin wayewa acikin industiri. Yayi wannan bayani ne acikin hirar da akayi da shi acikin Mujalla Fim ta wannan watan. Acewar Sani Danja: “Tabbas, akwai karanchi dama rashin wayewa acikin industiri, domin yawan hawa motoci da yawan saka sababbin kaya masu karin guga bashi ne yake nuna akwai wayayyu a industiri ba.

Ita wayewa tana nufin sani akan al’amura daban-daban bawai saka kaya masu kyau ba, saka kaya masu kyau tsafta yake nufi ba wayewa ba.” “Da yawan jaruman da suke industiri basu da hadin kai, domin basu waye da amfani gamida mahimmancin hadin kai ba.
kowa idan ya shigo industiri buri yake yafi dan uwansa suna da tarin kudi a kannywood.” Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa ya cigaba yana mai cewa tabbas, wannan tsantsar rashin wayewane. Akasashen da suka ci gaba kuma suka waye ba haka suke gudanar da harkar fim ba. haduwa suke suyi aiki tare su gudu tare su tsira tare amma mu ba haka bane a industiri inji Sani Danja.

The post DANDALIN KANNYWOOD: KARANTA KAJI ABINDA SANI DANJA YACE GAME DA RASHIN WAYEWAR ‘YAN FIM appeared first on MUJALLARMU.

KARANTA KAJI: INYAMURAI MASU FAFUTIKAR BIAFRA SUN MAKA BURATAI KOTU A KASAR AMURKA

$
0
0

Masu fafutuka Inyamurai sun maka Buratai a gaban kotu a kasar Amurika.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Wasu mutane 10,masu Fafutukar tabbatar da kasar Biyafara sun kai babban hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai kara gaban wata kotu dake kasar Amurika.
Masu gabatar da kara sun zargi Buratai da kama wasu mutane 13 da hannu wajen ganawa masu fafutukar tabbatar da kasar Biyafara azaba da kuma aikata kisan kai.
         
Wasu mutane 10,masu Fafutukar tabbatar da kasar Biyafara sun kai babban hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai kara gaban wata kotu dake kasar Amurika.
Masu karar suna son abiyasu diyar miliyoyin daloli na wahalar da suka sha da kuma asarar rayukan yan uwansu da sukayi.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa a wani taron manema labarai da suka gudanar a Jihar Legas, wasu kungiyoyin fararen hula sunyi zargin cewa anaso ayi amfani da masu karar ne domin a sanya gwiwowin jami’an suyi sanyi a yunkurin da suke na tabbatar da tsaro a kasarnan.

The post KARANTA KAJI: INYAMURAI MASU FAFUTIKAR BIAFRA SUN MAKA BURATAI KOTU A KASAR AMURKA appeared first on MUJALLARMU.

HAJJIN BANA: MANIYYATAN FILATO 400 SUN KASA BIYAN KUDADEN SU

$
0
0

Hajjin Bana: Maniyyatan Filato 400 Sun Kasa Biyan Kudaden Su.

                         Hajjin Bana: Maniyyatan Filato 400 Sun Kasa Biyan Kudaden Su

Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Filato ta ce cikin maniyyata 4oo daga cikin 600 da suka farayin adashen aikin haji na bana daga jihar sun kasa biyan kudaden su.

A yanzu haka hukumar ta ce mutane 200 ne kawai suka iya kamala biyan kudadensu.

Wani babban jami’in hukumar Wada Haruna, ya ce har yanzu gwamnatin jihar bata tsayar da ranar da zata rufe karban kudaden maniyyan da basu karasa biya ba.

Ya ce gwamnati ta ba jihar kujeru 1200 ne a hajin bana sannan Fulani makiyaya ne suka fi yawa cikin maniyyatar jihar.

The post HAJJIN BANA: MANIYYATAN FILATO 400 SUN KASA BIYAN KUDADEN SU appeared first on MUJALLARMU.

WASANNI: KARANTA KAJI SUNAYEN JIGA JIGAN ‘YAN WASAN REAL MADRID 6 DAKE SHIRIN CANZA SHEKA

$
0
0

Wasanni: Karanta jiga-jigan yan wasa 6 da ke shirin barin kungiyar Real Madrid.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Real Madrid ta yi fice wajen sayen ‘yan wasan kwallon kafa mafiya tsada a duniya, sai dai wannan karon ita ce za ta karbi makudan kudin da ake zawarcin ‘yan wasanta. – Watakila ‘yan kwallon Real Madrid shida ne ake sa ran za su sauya sheka da zarar an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan kwallon kafa ta bana.
                   
Cikin ‘yan kwallon da ake hasashen za su bar Santiago Bernabeu sun hada da Fabio Coentraro da Pepe da James Rodriguez da Alvaro Morata da Diego Llorente da kuma Mariano Diaz.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa shi Coentraro ana rade-radin Sporting Lisborn zai koma taka-leda aro, Pepe kuwa yarjejeniyarsa ce za ta kare a karshen watan Yuni, kuma kila Paris zai koma buga tamaula.
Sauran ‘yan wasa hudun da suka rage a nan ne Real Madrid za ta karbi kudin da ake cewa zai kai Yuro miliyan 160.
Madrid ba ta son sayar da Morata wanda Manchester United ke zawarci kan kudi kasa da Yuro miliyon 90, haka kuma kungiyar na sa ran samun Yuro miliyan 70 kudin James Rodriquez. Real Sociedad na zawarcin Llorente kan Yuro miliyan 8, shi kuwa Mariano Diaz zai iya barin Barnabeu kan Yuro miliyan 5.

The post WASANNI: KARANTA KAJI SUNAYEN JIGA JIGAN ‘YAN WASAN REAL MADRID 6 DAKE SHIRIN CANZA SHEKA appeared first on MUJALLARMU.

KUNJI: ZA BIYA KUSAN NAIRA MILIYAN 2 GA MUTUMIN DA YARDA AKA SAKA MASA CUTAR TARIN FUKA DA GANGAN SABODA GWAJIN KIMAYYA-(Karanta)

$
0
0

Shin nawa za a biya ka?, don a yaɗa maka tarin fuka da gangan saboda gwajin kimiyya? Masu bincike a Jami’ar Southampton ta Ingila na tayin ba da ladan fam 3,526 kusan naira miliyan biyu kan wannan ƙalubale.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Suna son yin wani ingantaccen riga-kafi don kare jarirai da yara ‘yan dagwai-dagwai har ma da manyan da ke cikin kasadar kamuwa da wannan cuta. – Don samun wannan dama, sai shekarun mutum sun kai 18-45 kuma sai mai ƙoshin lafiya wanda zai so zama a wani keɓantaccen wuri tsawon kwana 17 yana rera waƙa.
      
Tarin fuka, wata cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar tofar da yawu ko tari daga mutanen da suka kamu.
Ayarin ƙwararru a Southampton na son yaɗa wa mutane masu ƙoshin lafiya ƙwayar wannan cuta (ta hanyar ɗora ƙwayoyin bakteriyar da ake kira pertussis a kan hancinsa) don ganin yadda za su wanye.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa wasu daga cikin ‘yan sa-kan za su kamu da rashin lafiya, amma masana kimiyyar sun fi mayar da hankali a kan waɗanda ba a ga kowanne nau’i na alamomin cutar a jikinsu ba, duk da yake, ƙwayar cutar ta shige su ta hanci.
Abin da suke nema a nan shi ne masu ɗauke da cutar a fakaice, da kuma mutanen da tun ainihi suna da kariyar wannan cuta mai yaɗuwa. Za a biya kusan N2miliyan ga wanda ya yarda a sa masa cuta Za a biya kusan N2miliyan ga wanda ya yarda a sa masa cuta Mutanen da ke ɗauke da cutar a fakaice suna yaɗa cutar tarin fuka ga wasu, amma dai su kuma ba ta sa su rashin lafiya ba.
Ga alama suna da isasshen garkuwar cutar tarin, duk da yake ba a yi musu riga-kafi ba. Akwai mutane ƙalilan, waɗanda su kwata-kwata ba sa kamuwa.
Fahimtar hakan za ta taimaka wajen ƙirƙiro wani riga-kafi mai matuƙar inganci. Jagoran masu binciken, Farfesa Robert Read na cewa:
“Muna son sanin wacce irin baiwa ce da su, kuma me ya sa ba za mu iya harbarsu da cutar ba, har su dinga yaɗa ta a fakaice.”

The post KUNJI: ZA BIYA KUSAN NAIRA MILIYAN 2 GA MUTUMIN DA YARDA AKA SAKA MASA CUTAR TARIN FUKA DA GANGAN SABODA GWAJIN KIMAYYA-(Karanta) appeared first on MUJALLARMU.


MUN GAJI DA GAFARA SA: A FITO FILI A FADA MUNA GASKIYA SHIN SHUGABA BUHARI YA MUTU NE KO YANA RAYE?-Inji Fani Kayode

$
0
0

 Babu mamaki ma Buhari ya mutu – Fani-Kayode

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Femi Fani-Kayode ya ce kila shugaba Muhammadu Buhari ya mutu -Ya kalubalanci fadar shugaban kasa da ta daina yawo da hankalin jama’a ta filo fili ta bayyana gaskiya a kan halin da yake ciki Ya kuma ce a kawo hujja da zai tabbatar da cewa yana nan da ransa bai mutu ba kamar yadda suke ikirari Tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayose ya ce babu mamaki kila ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu.
     
Hakan na kunshe ne a cikin sabon labara da ya aika ma jaridar Daily Post a safiyar ranar Juma’a. Ya ce kunbiya-kunbiya da fadar shugaban kasa keyi ya sa ‘yan Najeriya cikin rashin kwanciyar hankali sannan kuma yasa suka kalubalanci gwamnati da ta saki hotunan shugaban kasar.
Babu mamaki ma Buhari ya mutu – Fani-Kayode Babu mamaki ma Buhari ya mutu inji Fani-Kayode
Tsohon kakakin shugaban kasar y ace: “Fadar shugaban kasa ta bayyana mana cewa Buhari ya yi tafiya zuwa wajen kasar amma har yanzu babu wanda ya hotuna ko sahun sa a lokacin da ya ke barin Najeriya ko kuma lokacin da ya isa kasar wajen da aka ce. “Misali a ce da gaske ya yi tafiya muna al’ajabin wacce kasa aka kais hi, da kafa ya je ko da bayan sa sannan kuma shin yana a asibiti ne ko kuma yana wani kebantaccen guri ne.
“Fadar shugaban kasar ta yi ikirarin cewa yana raye har yanzu sannan kuma muna sa ran cewa Allah ya sa haka zancen ya ke. “Babu yarda a tsakanin masu mulki da wadanda ake mulka a Najeriyarmu ta yau.
“Maganar shine: Idan shugaban kasar ya mutu, a daina wasa da hankulan jama’a, a fada mana gaskiya, a binne shi da daraja sannan a bari ruhinsa ya huta. “Idan kuma yanba raye a bari mu san ainahin abun da ke damun sa, halin da yake ciki, inda yake, yadda yake, sannan kuma mafi muhimmanci a nuna mana hujjar yana raye’, Inji Fani-Kayode.

The post MUN GAJI DA GAFARA SA: A FITO FILI A FADA MUNA GASKIYA SHIN SHUGABA BUHARI YA MUTU NE KO YANA RAYE?-Inji Fani Kayode appeared first on MUJALLARMU.

KWANAKI 10 KAFIN SALLAH SANATOCI SUN JE HUTUN SALLAH

$
0
0

    Ramadan: Kwanaki 10 kafin Sallah, Sanatoci sun tafi hutu.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

A yau, kimanin kwanaki 10 kenan kafin Sallah, Sanatoci sun fara hutu – Sanatocin sun debi hutun satuka guda 3 ne A ranar Alhamis 15 ga watan Yuni ne yan majalisar dattawa suka dage zaman majalisa har sai bayan satuka guda uku, domin yin hutun karamar Sallah da kuma na murnar cikarsu shekaru 2.
Jaridar Daily Post ta ruwaito a ranar juma’a 9 ga watan Yuni ne dukkanin majalisun biyu, na wakilai da dattawa suka cika shekaru 2 cig cif da kama madafan iko, inda kuma suma gudanar da wata yar kwarya kwaryar zama domin murnan wannan rana.
Zaman ya samu halartan jiga jigan majalisar daga dukkanin bangarorin biyu, kamar yadda majiyar Dandalin Mujallarmu.com ta kalato.
Sanatoci Bugu da kari dayake ana sa ran a ranakun 25 da 26 ne za’a yi bikin karamar Sallah bayan watan Ramadana, yan majalisun sun tattara hutun nasu har sai bayan sallar.
Bayan kammala zaman majalisar ne, sai shugaban masu rinyaje, Ahmad Lawan ya gabatar da kudirin dage harkokin majalisa har sai bayan sati uku, daga nan kuma shugaban marasa rinjaye Akpabio ya mara masa baya.
Shikenan sai shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki ya buga guduma, alamar an tashi zaman kenan.

The post KWANAKI 10 KAFIN SALLAH SANATOCI SUN JE HUTUN SALLAH appeared first on MUJALLARMU.

SHUGABA BUHARI NA NAN DA RAI BAI MUTU BA,KULLUM ANA MAGANA DASHI-Inji Lai Muhammad

$
0
0

Buhari na nan da rai da lafiya, Osinbajo na magana da shi kulli yaumin – Lai Mohammed .

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

         
Sabanin jita-jitan da ke yaduwa cewa shugaba Buhari yayi wafati a kasar Ingila, ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, yace mukaddashin shugaban kasa na magana da shi kulli yaumin. Ya bayyana wannan ne a Legas a wata hira da gidan Talabijin Channels mai suna Siyasar yau.
Game da cewar Lai Mohammen, Buhari yayi matukar yarda da Osinbajo kuma yana biyayyansa sosai. Yace: “ Mukaddashin shugaban kasa na tattaunawa da shugaban kasa saboda haka inada yakininc cewa shugaban kasan na da cikakkaen masaniya game da abubuwan da mukaddashin shugaban kasan keyi kuma akwai yarda tsakaninsu kuma ban tunanin wannan matsala ne.
” Akan zancen garambawul, Lai Mohammaed yace wannan ba wani abun da ya kamata mu mayar da hankalinmu kai bane a yanzu.
Yace: “Nayi bayani a wurare daban-daban cewa abin da ke gaban wannan gwamnati shine zaman lafiya. “Abin da ke gabanmu shine farfado da tattalin arzikin Najeriya da kuma yaki da rashawa saboda karfafa guiwan wannan kasa. “Zamu iya maganan garambawul daga baya amma ba yanzu ba gaskiya.”

The post SHUGABA BUHARI NA NAN DA RAI BAI MUTU BA,KULLUM ANA MAGANA DASHI-Inji Lai Muhammad appeared first on MUJALLARMU.

WASANNI: RONALDO NA SHIRIN BARIN REAL MADRID KUMA YA BAYYANA INDA ZAI KOMA

$
0
0

Ronaldo na neman barin Real Madrid ya kuma bayyana inda zai koma.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Ba mamaki Tauraron Kungiyar Real Madrid zai bar kulob din kwanan nan Babban Dan wasa Cristiano Ronaldo na shirin komawa Man Utd Ronaldo bai ji dadin yadda aka budo masa wuta game da maganar haraji ba Kuna da labari cewa ana zargin Babban Dan wasa Ronaldo da rashin biyan haraji.
            
Dan wasan bai ji dadin wannan abu ba ya kuma shirya barin Kulob din. Babban Dan wasan yace so yake ya koma Kungiyar Manchester United.
Ronaldo na neman barin Real Madrid ya kuma bayyana inda zai koma Ronaldo zai koma kulob din sa na da? Rahotanni daga Kasar Sifen na nuna cewa Tauraron Dan wasan Kungiyar Real Madrid na shirin tashi bayan an fusata sa game da zargin kin biyan haraji a Kasar.
              
Ana zargin ‘Dan wasan da kin biyan kusan Dala Miliyan 16 ga Hukuma,Ronaldo na so koma Kungiyar Manchester Unite Ronaldo ya bayyana cewa zai so ya koma Kungiyar sa ta da watau Manchester United ta Ingila inda yace yake da abokan da ya shaku da su.
Ronaldo dai na ganin Real Madrid ta yi watsi da shi a cikin yanayin da yake ciki asali ma an yi tallar riga ba tare da shi ba. Kun ji jiya cewa Shugaban Kungiyar kwallon kafan kasar Faransa Noel Le Graet yace wata rana Koci Zinedine Zidane na Real Madrid zai horar da Kasar Faransa.

The post WASANNI: RONALDO NA SHIRIN BARIN REAL MADRID KUMA YA BAYYANA INDA ZAI KOMA appeared first on MUJALLARMU.

KARANTA KAJI: DALILIN DAYASA SARKIN KANO SANUSI II YA KAIWA YEMI OSINBAJO ZIYAR A FADAR SHUGABAN KASA

$
0
0

Dalilin Da Yasa Sarkin Kano Ya Kaiwa Mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo Ziyara

                   Dalilin Da Yasa Sarkin Kano Ya Kaiwa Mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo Ziyara
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar fadar gwamnatin tarayyar Nijeriya da ke Aso Villa, Abuja, inda ya yi ganawa ta sa’o’i biyu da mukaddashin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo

Bayan kammala tattaunawar, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ki bayyanawa manema labarai dalilinsa na zuwa ganin Osinbajo da kuma abubuwan da suka tattauna, sai dai Kamfanin dillancin labarai ta Nijeriya NAN ta samo wannan dalilin ziyarar ta Sarki Sanusi daga majiya mai tushe.

 

NAN ta bayyana cewa Sarki Sanusi ya yi kafa da kafa ne don ya jaddada godiyarsa ga Farfesa Osinbajo bisa saka baki da ya yi wajen tsayar da binciken masarautar Kano da majalisar dokokin jihar ta fara kan zargin masarautar da Sarki da wasu laifuka har guda 8, wanda daga ciki har da yin “wa kaci ka tashi da dukiyar masarauta”

In baku manta ba dai majalisar ta Kano ta dakatar da binciken nata ne sakamakon wata takarda da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya rubuta wa zauren majalisar yana mai hakurkurtar da ‘yan majalisar

Takardar da kakakin majalisar ta Kano, Rayit Honarabul Kabiru Rurum ya karanta a zauren majalisar ta bukaci da majalisar ta Kano da ta dakatar da binciken Sarki da masarauta musamman saboda wasu manyan kasar nan da suka bukaci da a yi hakan

Gwamna Ganduje ya bayyana wa majalisar sunayen wadanda suka nemi gwamnan da ya sanya baki wajen dakatar da binciken wanda cikinsu akwai: Mukaddashin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Shugabannin jam’iyyar APC, Tsofaffin shugabannin Nijeriya, Janar Ibrahim Babangida da Abdussalamu Abubakar, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, manyan ‘yan kasuwa Aliko Dangote da Aminu Dantata

NAN gathered that the Emir’s visit to the Presidential Villa might also be part of the ongoing consultations by the acting president with stakeholders which began with foremost Leaders of thought from the Northern and South East States of the federation.

NAN ta bayyana cewa ziyar ta Sarki Sanusi har ila yau na da alaka da batun tattaunawa da masu ruwa da tsaki na yankunan Arewa da na Kudu maso gabashin Nijeriya

The post KARANTA KAJI: DALILIN DAYASA SARKIN KANO SANUSI II YA KAIWA YEMI OSINBAJO ZIYAR A FADAR SHUGABAN KASA appeared first on MUJALLARMU.

KURA KURAN SHUGABA BUHARI NE SUKA TSAYAR DA DUKIYAR KASA CAK-Inji Reno Omokri

$
0
0

‘Kura-kuran Buhari ne suka durkusar da Najeriya’ – Reno Omokri.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Buhari ya kashe ayyuka miliyan 4 a wata uku Ya tsayar da dukiyar kasa cak Ya talauta Najeriya dare daya – Buhari yayi satar amsa daga tsohon shugaba Jonathan.
               
A sabuwar caccaka da ya saba fitarwa kusan kullum kan gwamnatin APC, Reno Omokri, tsohon hadimin shugaba Jonathan mai zama a Amurka, ya ce dare daya Buhari ya talauta Najeriya, saboda kawai ya matsu ya nuna bajintarsa.
A cewarsa, yana hawa mulki, shugaba Buhari ya dauki matakin kwakkwashe duk kudin kasa ya boye a babban bankin Najeriya, na CBN, inda ya talauta dukkan ma’aikatu. Wannan shine ummul-aba’isin durkushewar Najeria dare daya.
A cewar Reno, shawarar tare dukiyar kasa wuri daya ta tsohuwar ministar kudi ne, Okonjo-Iweala, da Goodluck Jonathan, amma su a hankali suke niyyar yi ba dare daya ba. “Kwashe kudaden, shi ya kawo durkushewar Najeriya dare daya, ya kuma kawo korar ma’aikata miliyan hudu da rabi,” inji shi.
A cewarsa, hukumar kididdiga ta kasa ta bayar da kiyasin rasa ayyukan yi har dubu hamsin daga bankuna kadai, saboda kudadensu na kasuwanci da aka kwashe.
An dai sami matsalolin tattalin arzikin kasa sosai a shekaru biyu na mulkin APC.

The post KURA KURAN SHUGABA BUHARI NE SUKA TSAYAR DA DUKIYAR KASA CAK-Inji Reno Omokri appeared first on MUJALLARMU.

TIRKASHI: DADIN ZAMA DA ‘YAN BOKO HARAM YASA WATA BUDURWA DA AKA CETO TA KOMAWA TSOHON MIJINTA DAN BOKO HARAM

$
0
0

Tirkashi! Wacce aka ceto daga hannun Boko Haram ta tsere ta koma wajen mijinta dan Boko haram.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Matar wani kwamandan Boko Haram, Aisha, da aka ceto ta tsere daga gidansu da ke Maiduguri ta koma wajen mijinta dan Boko Haram da ke dajin Sambisa.
Kana ta tafi da yarin da haifa ma dan Boko Haram din mai suna Mamman Nur. Ta arce ne bayan fitowa daga shirin gwamnatin tarayya na wayar musu da kai bayan an cetosu daga hannun Boko Haram. Yar uwarta, Bintu Yerima, ta bayyana cewa Aisha ta kwashe kayayyakinta ne bayan ta amsa wani kira a waya.
           
Tace: “Kafin ta tafi, ta amsa wayan wata mata wacce ke tare da ita a shirin. Maan tace sun koma dajin Sambisa”.
Bintu tace bayan arcewanta, Aisha ta ki amsa wayanta, a karshe ma kashe wayan tayi.
Wata masaniyar tunanin dan Adam, Fatima Akilu tace da ta samu labarin wasu yan mata sun koma wajen Boko Haram, ta lura da cewan wasunsu na son komawa saboda dadin da suke ji da kuma kunyan da suke ji cikin jama’a da kyama.

The post TIRKASHI: DADIN ZAMA DA ‘YAN BOKO HARAM YASA WATA BUDURWA DA AKA CETO TA KOMAWA TSOHON MIJINTA DAN BOKO HARAM appeared first on MUJALLARMU.


MIJI YA NEMI KOTU TA RABA AUREN SA DA MATAR SA SABODA TA JIBGAN SA KODA YAUSHE

$
0
0

Mata ta na jibga ta a duk lokacin da ta ji sha’awan yin haka – Inji Mijin tace.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Toafeek Giwa ya koka ma wata kotun gargajiya dake zamanta a garin Agodi, jihar Ibadan,Toafeek Giwa ya nemi da’a raba aurensu da matarsa Abiodun Omotayo Wani dan fansho Toafeek Giwa ya koka ma wata kotun gargajiya dake zamanta a garin Agodi, jihar Ibadan, inda ya nemi da’a raba aurensu da matarsa Abiodun Omotayo.
       
Taofeek ya shaida ma kotu a ranar juma’a 16 ga watan Yuni, cewar matar tasa na jibgarsa ne ba kakkautawa ko da laifi ko ba laifi, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.
A jawabinsa, Taofeek yace “Abu kadan sai kaga ta shiga jibga ta, har da yaga min riga, a yan kwanakin nan ma guba ta sanya min cikin abinci na, alhali kuma ban shirya mutuwa yanzu ba.
Don haka nake bukatar kotu ta raba auren mu kafin ta kashe ni, domin in kula da yara na” Mata ta na jibga ta a duk lokacin da ta ji sha’awan yin haka – Inji Mijin tace Kotuu Da take kare kanta, Uwargida Omotayo, ta musanta dukkanin zarge zargen da mijin nata yayi, inda tace asali ma mijin nata ne ke yawan binta da adda zai kashe ta, sa’annan tayi amanna da a raba auren, amma ta roki da bata dansu guda daya rak da suka haifa.
Ba tare da bata lokaci ba, kotu ta raba auren, sa’annan ta bata rikon dan nasu, daga bisani kotu ta umarci mijin daya baiwa matar N3000 duk wata domin kulawa da yaron nasu.

The post MIJI YA NEMI KOTU TA RABA AUREN SA DA MATAR SA SABODA TA JIBGAN SA KODA YAUSHE appeared first on MUJALLARMU.

HUKUNCIN BARIN MATA ZUWA MASALLACI A GOMAN KARSHE NA RAMADAN DOMIN GABATAR SALLAR TAHAJJUD

$
0
0

Hukuncin Fitar Mata Zuwa Masallaci A Goman Karshe Na Ramadan Don Gabatar Da Qiyaamu Ramadan

Hukuncin Fitar Mata Zuwa Masallaci A Goman Karshe Na Ramadan Don Gabatar Da Qiyaamu Ramadan

1. Sunnah ce wacce ake son aikatawa: Mata Musulmi su fito Masallatai su yi Qiyaamu Ramadan a goman karshe cikin jam’i.
Imam Ibnu Khuzaimah wanda yau da mutuwarsa shekaru dubu daya da dari daya da ishrin da bakwai (1,127) ya ce cikin sahihinsa mai suna Mukhtasarul Mukhtasar 3/339: ((باب استحباب صلاة النساء جماعة مع الامام في قيام رمضان مع الدليل على ان قيام رمضان في جماعة أفضل من صلاة المرء منفردا في رمضان)).

 

Ma’an((Babin mustahabbancin sallar mata a cikin jam’i tare da Liman a cikin Qiyaamu Ramadan, da kuma hujjar cewa yin Qiyaamu Ramdan a cikin jam’i shi ne ya fi a kan mutum ya yi salla shi kadansa cikin Ramadan)).

 

Sheikh Hamzah Bin Faayee ya ce cikin littafinsa Talaa’i’us Sulwaan shafi na 138 ((فالخلاصة ان خروجهن للتراويح مسنون ومحمود )). Ma’ana: ((A takaice dai lalle fitowarsu saboda yin sallar Taraawiihi sunna ce kuma abin godewa)).

 

2. Hujjar mustahabbancin fitowar Mata Masallatai domin sallatar Qiyaamu Ramadan cikin jam’i a goman karshe shi ne: Hadithin Sahabi Abu Zarr Hadithi na 1377 cikin Abu Dawud, na 806 cikin Tirmizii, na 1364 cikin Nasaa’ii, na 1327 cikin Ibnu Majah, na 21,447 cikin Musnadu Ahmad, na 2206 cikin Sahihu Ibnu khuzaimah, na 4042 Musnadu Bazzar, na 7706 cikin Musannafu Abdirrazzaq cewa shi Abu Zarr ya ce:-

((صمنا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم رمضان فلم يقم بنا شيءا من الشهر حتى بقي سبع فقام بنا حتى ذهب ثلث الليل فلما كانت السادسة لم يقم بنا، فلما كانت الخامسة قام بنا حتى ذهب شطر الليل، فقلت يا رسول الله! لو نفلتنا قيام هذه الليلة؟ قال: فقال: ان الرجل اذا صلى مع الامام حتى ينصرف حسب له قيام ليلة. قال: فلما كانت الرابعة لم يقم، فلما كانت الثالثة جمع أهله ونساءه والناس فقام بنا حتى خشينا ان يفوتنا الفلاح)).

Ma’ana: ((Mun yi azumin Ramadan tare da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah bai mana limancin kome ba a sallar qiyaamul laili cikin watan sai da ya rage kwana bakwai watan ya kare sai ya yi mana limancin qiyaamul laili saida kashi daya cikin na dare ya tafi, a dare na shida da ya rage bai yi mana limancin qiyaamul laili ba, a dare na biyar da ya rage sai ya yi mana limancin qiyaamul laili har saida rabin dare ya tafi, to sa na ce: Ya Manzon Allah! Me ya sa ba ka yi mana qiyaamul lili na dukkan daren ba? Sai ya ce: Hakika idan mutum ya yi salla tare da liman har dai limamin ya gama sallar to kuwa za a ba shi ladan wanda ya sallaci dukkan daren ne. Ya ce: a dare ba hudu da ya rage bai yi mana limancin qiyaamul laili ba, a dare na uku da ya rage sai ya taro iyalansa, da matansa na aure, da kuma mutane ya yi mana limancin qiyaamul laili har saida muka ji tsoron kada yin sahur ya kubuce mana)). Wannan Hadithi Albaanii da sauransu sun inganta shi.

 

– Ya zo cikin riwayar Tirmizii ((Ya kira iyalansa, da matansa na aure ya yi mana limancin qiyaamul laili)).
– Ya zo cikin riwayar Nasaa’ii ((Sai ya aika zuwa iyalansa, da matansa na aure, ya tara mutane ya yi mana limancin qiyaamul laili)).
– Ya zo cikin riwayar Bazzar ((Sai ya aika zuwa ga iyalansa, da matansa na aure suka hadu sannan ya yi mana limancin qiyaamul laili)).
– Ya zo cikin riwayar Abdirrazzaq ((Ya aika zuwa ga iyalansa mutane kuma suka taru sannan ya yi kana limancin qiyaamul laili)).

 

3. Ke nan tunda cikin sashin wadannan goman karshen Annabi mai tsira da amincin Allah ya tara iyalansa da matansa na aure da kuma sauran jama’a a cikin masallacinsa ya yi musu limancin qiyaamul laili, wannan yana tabbatar mana da cewa lalle maza da mata su taho masallaci a darairan goman karshe domin yin qiyaamu Ramadan cikin jima’i shi ne ya fi falala,shi ne abin so; saboda shi ne Annabi Mai tsira da amincin Allah ya zaba wa al’ummarsa; shi kuwa Annabi mai tsira da amincin Allah ba ya zaba wa al’ummarsa wani abu sai in abin shi ne ya fi falala a gurin Allah Madaukakin Sarki.
Ibnu Qudaamah ya ce cikin Al-Mugni 7/334 :-
((ولا يشتغل النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه الا بالافضل)).

 

Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah da sahabban shi ba sa shgalta sai da abin da shi ne ya if falala)).
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin majmuu’ul Faawaa 26/54:-
((والنبي صلى الله عليه وسلم لا ينقلهم من الفاضل الى المفضول بل إنما يأمرهم بما هو أفضل لهم)).

Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ba zai cirar da su daga abu mai daraja ba zuwa ga abin da aka fi shi daraja, a’a ya kan umurce su ne da abin da shi ne mafi falala gare su)).

 

4. Idan wani ya kalubalanci wannan magana tamu ya ce: ai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce ((Mafificiyar salla ita ce sallar mutum a cikin dakin shi matukar dai ba sallar farilla ba)). Sai mu ce da shi wannan Hadithi an toge shi da hadithin Abu Zarr da muka ambata a sama, kamar yadda aka toge shi aka khassase shi da Hadithan sallar Idi, da rokon ruwa, da kusuufin Rana.  Watau sai a ce: sallar nafila a gida ita ta fi falala amma banda nafilfilin qiyaamu Ramadan a daren goman karshe, banda nafilfilin sallar Idi, da rokon ruwa, da khusufin Rana….

 

5. Idan kuma wani ya kalubalance mu cikin abin nan da muka fada ya ce: ai Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Kada ku hana mata zuwa masallatai, amma kuma dakunansu su ne suka fi alheri a gare su)). Sai mu ce da shi wannan Hadithi an toge shi watau an khassase shi da hadithin Abu Zarr da muka ambata a sama kamar yadda aka khassase shi da hadithin umurtan mata da su fita zuwa masallacin Idi: masu tsarkinsu da mara tsarkinsu. Watau sai a ce: Mata su yi sallolinsu cikin dakunansu shi ne ya fi falala a gurin Allah matukar dai sallolin nan ba na Idi ba ne, matukar dai sallolin nan ba na qiyaamu Ramadan ba ne a dararen goman karshe.

Allah Ya taimakemu. Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata. Ameen.

 

Sheikh Dakta Ibrahim Jalo Jalingo

The post HUKUNCIN BARIN MATA ZUWA MASALLACI A GOMAN KARSHE NA RAMADAN DOMIN GABATAR SALLAR TAHAJJUD appeared first on MUJALLARMU.

TOH FA: NI ZAN ZAMA SHUGABAN KASA BAYAN SHUGABA BUHARI-INJI FAYOSE

$
0
0

    Ni Zan Zama Shugaban Kasa Bayan Buhari – Fayose

 

Gwamnan jahar Ekiti Ayodele Fayose a jiya Juma’a ya bayyana aniyar sa na zama shugaban kasar Nijeriya idan Buhari ya sauka a 2019.

A cewar sa “Na saba kwace mulki daga hannun mutane. Wannan da ke hannun Buhari ma zan karba. Daga nan Villa zan shiga. Ni ne shugaban kasar Nijeriya na gaba”

Ya ci gaba da cewa “Ina son na zama shugaban kasar Nijeriya. Nawa canjin ba zai kasance irin wannan da aka kasa ganin komai a kasa ba. Za mu wakilci jama’a ne mu kuma fada masu gaskiya.

Fayose dai ya na magana ne bayan wata ganawa da gwamnonin jam’iyyar PDP suka yi a Jahar Ekiti

The post TOH FA: NI ZAN ZAMA SHUGABAN KASA BAYAN SHUGABA BUHARI-INJI FAYOSE appeared first on MUJALLARMU.

ABIN KUNYA: AN KORI WANI INSIFETON ‘YAN SANDA DAGA AIKI SAKAMAKON YIWA WATA YARINYA ‘YAR SHEKARA 15 FYADE

$
0
0

An kori wani Insifeto daga aikin dan sanda sakamakon yi wa wata yar shekaru 15 fyade.

Marubici:Haruna Sp Dansadau

Rundunar Yan sandan Nijeriya ta fatattaki wani insifeto dan sanda daga aiki mai suna Joseph Etuk sakamakon yiwa yarinya ‘yar shekaru 15 Fyade a jihar Akwa Ibom. Ofisan yada labarai na rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, Mr Chukwu Ikechukwu ya bayyana cewa Etuk na aiki a ofishin ‘yan sandan dake Mkat Enin a jihar Akwa Ibom kuma ya samu labarin an fatattake shi daga aiki tun a watan Afrilu bayan ya aikata fyade ga wata yar sakandare Mary Udo da nuna mata bindiga a yayin da take dawowa da Coci a unguwar Mkat Enin.

Dandalin Mujallarmu.com ta samu a wani labarin kuma cewa Wani ma’akaci da yayi ritaya Taofeek Giwa ya roki kotun gargajiya ta Idi-Ogungun dake Ibadan kan taraba aurensa da matarsa Abiodun Omotayo,kan cewa tana dukansa a duk lokacin da taga dama.

The post ABIN KUNYA: AN KORI WANI INSIFETON ‘YAN SANDA DAGA AIKI SAKAMAKON YIWA WATA YARINYA ‘YAR SHEKARA 15 FYADE appeared first on MUJALLARMU.

KARANTA KAJI: DAGATACCEN DAN MAJALISA JIBRIN ABDULMUMINI YASA GSAR NAIRA MILIYAN 2 AKAN ZANEN HOTUN SHUGABA BUHARI DA IYALAN SA

$
0
0

Dakataccen dan majalisa Abdulmumini ya sa gasar naira miliyan 2 akan zanen hoton Buhari.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Abdulmuminu Jibrinya sa gasa akan zanen hoton shugaban kasa Muhammadu Buhari – Mutane da dama masu amfani da shafin Facebook da Instgram sun shiga amma mutane 20 ne suka yi nasara Dakataccen dan majalisar wakilai Abdulmuminu Jibrin Kofa ya sa gasa akan zanen hoton shugaban kasa Muhammadu Buhari da iyalansa.
                   
Gasar wacce mutane da dama masu amfani da shafin Facebook da Instagram suka shiga amma mutane 20 ne suka yi nasara kowane ya samu kyautar Naira 100,000. KU
Gwamnan APC ya bayyana Dakataccen dan majalisa Abdulmumini ya sa gasar naira miliyan 2 akan zanen hoton Buhari
                 
Jibrin ya nemi kowa ya bayyana manufa mai kyau dangane da zanen a matsayin nuna kauna ga Buhari.
A cewar sa mutane da dama sun yi ta ikirarin cewa zanen Mallakin su ne amma daga baya an gano ainihin mai zanen dan kasar Ghana ne mazaunin Amurka mai suna Kwadwo Bediako, mai kamfanin “Penciled Celebrities”.

The post KARANTA KAJI: DAGATACCEN DAN MAJALISA JIBRIN ABDULMUMINI YASA GSAR NAIRA MILIYAN 2 AKAN ZANEN HOTUN SHUGABA BUHARI DA IYALAN SA appeared first on MUJALLARMU.

Viewing all 3050 articles
Browse latest View live


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>