Dalilai 6 da ke hana mutane taimakawa da jininsu a asibitocin Najeriya.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau

The post KARANTA KAJI: DALILAI 6 KWARARA DAKE HANA MUTANE TAIMAKAWA DA JININ SU A ASIBITOCIN NIJERIYA? appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
The post KARANTA KAJI: DALILAI 6 KWARARA DAKE HANA MUTANE TAIMAKAWA DA JININ SU A ASIBITOCIN NIJERIYA? appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
The post DANDALIN KANNYWOOD: INA MURNA DA DAWOWAR RAHAMA SADAU A HARKAR FIM DIN HAUSA-Inji Aisha Tsamiya appeared first on MUJALLARMU.
Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa ba za ta baiwa shugaba Muhammadu Buhari damar zarcewa a matsayin dan takara daya tilo da babu hamayya ba a zaben shekarar 2019
Shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso yamma, Malam Inuwa Abdulkadir ne ya bayyana hakan inda ya ke cewa za a fafata tsakanin ‘yan takarkari masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben fid da gwani na jam’iyyar APC kuma za a yi hakan da adalci ta yadda duk wanda ya yi nasara za a bashi damar ya tsaya a babban zaben 2019 don karawa da sauran jam’iyyu
Ya fadi hakan ne a lokacin da ya ke amsawa tambayoyi daga manema labarai, inda aka tambaye shin akwai damar wani dan jam’iyyar APC zai iya tsayawa takarar shugaban kasaa shekarar 2019?
Sai ya ce, “Tsari jam’iyyar shi ne za a bawa kowane dan takara damar tsayawa a zaben fid da gwani na jam’iyyar APC”
Ya ci gaba da cewa, to amma yanzu a shekarar 2017 muke, saboda haka masu neman wannan kujera ta shigaban kasa sai su bari sai lokaci ya yi
Ko dai Buhari zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019 ko ma ba zai sake tsayawa ba, lalle dai jam’iyya za ta gudanar da zaben fid da gwani saboda dai jam’iyyar APC hjam’iyya ce da ke gudanar da al’amuranta bisa tsarin dimokuradiyya
The post ZA FAFATA TSAKANIN BUHARI DA ‘YAN TAKARAR SHUGABAN KASA NA JAM’IYYAR APC A ZABEN FIDDA GWANI appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Gwamnatin jihar Kaduna ta hana hawa babur a wasu sashi na jihar – Hakan na da alaka da yawan sace mutane da akeyi don kudin fansa Mai bai wa Gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin tsaro, Kanal Yusuf Yakubu Soja, ya ce majalisar tsaro ta jihar ta haramta hawa babur a wasu garuruwa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin a samu sukunin yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa, kamar yadda ya ce.
Babban jami’in da ke kula da ayyukan yaki da miyagun ayyuka wato (Operation Yaki), ya ce sun dauki matakin ne bayan tattaunawa a majalisar tsaro ta jihar wadda ta samu halarcin sarakuna da kuma hakiman yankin da abin ya shafa.
Ya ce dokar za ta fara aiki ne daga garin Kakau zuwa Jere wadanda suke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Iliyasu Umar wani wanda yake sana’ar acaba ne a garin Jere, ya ce: “A gaskiya ba mu ji dadin daukar wannan matakin ba. Da wannan sana’ar mu ke ci, mu ke sha. Idan babu wannan sana’ar za mu koma gida mu zauna ke nan.” Ya ci gaba da cewa “yan acaba ba su da hannu a satar mutane don haka bai kamata a hana mu yin acaba ba.”
Hakazalika, Kanal Yusuf ya ce Babban Sufeton ‘Yan Sandan kasar ya aike da jami’an ‘yan sanda 600 wadanda za su rika yin sintiri a kan babbar hanyar don farauto masu garkuwa da mutane. Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin arewacin kasar da suke fama da matsalar satar mutane.
The post KARANTA KAJI: GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA HANA HAWA BABUR appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Barista Solomon Dalung ya ce ko shakka babu talakawa sune matsalar Najeriya – Yace duk sanda kaji wata matsala ko tashin hankali ya kunno kai to zaka samu talaka ne ya kirkiro ta Ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce ko shakka babu talakawa sune matsalar Najeriya.
Yace duk sanda kaji wata matsala ko tashin hankali ya kunno kai to zaka samu talaka ne ya kirkiro ta saboda talaka shine bai yadda da dan uwansa ba, kuma bai yadda da addinin wani ba sannan ga bakin ciki da hassada ga junansu.
Dalung ya bayyana haka ne a wajen taron cin abincin dare na shekara-shekara da hukumar UFUK Dialogue Foundation ta shirya a Abuja.
Sai dai babban limamin cocin katolika na Abuja, Archbishop, John Cardinal Onaiyekan, wanda shima yayi jawabi a wajen taron ya nuna jayayya da ra’ayin ministan.
A cewar Onaiyekan fitattun mashahurai da matsakaitan masu kudi sune matsalar Nigeria, yana mai cewa sune ke haddasa yawancin fitintunu.
The post KUNJI FA: TALAKA NE BABBAR MATSALAR NIJERIYA-INJI MINISTAN WASANNI SOLOMON DALUNG appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Muhawara na kara zafafa tsakanin kudu da arewar Najeriya – An ci gaba da hararar juna tsakanin kabilun kudu da arewa Anyi kira da kowa ya so juna tsakanin makwabta kabilu Cif Hope Uzodinma, sanata daga jihar Imo, a majalisar dattijai, na kabilar Ibo, ya baiwa kabilun kudu maso gabashin Najeriya shawara da su hakura su zauna a ajeriya, su girmama doka, su kuma bada irin tasu gudummawar don ci gaban kasa.
Ya yi wannan kiran ne a birnin landan na Ingila, inda a bagare daya kuma ya kira ga gwamnatin tarayya da ta ciyar da yankin na gabashin najeriya gaba, inda yayi kira da a taimaka wa yankin nasa a kafa musu wata babbar cibiya ta kere-kere wadda zata tafiyar da tattalin arzikin yankin, musamman ganin dama kabilar sun kware wajen kere-kere.
Sanatan na tsokaci ne a laccar da ya bayar kan ci gaban kabilar ibo a duniya, inda ya yi kira ga kabilar da su hakura da batun ballewa daga Najeriya, harma kuma ya buga misali da yan siyasar kabilar da suka yi fice a duniya da wasu kasashen dama iyaye dattijai da suka kafa kasar najeriya.
Karshen taron ya watse dai da alwashin da masu halartar taron sukayi, na sake nuna soyayyar su ga hadin kan Najeriya, da kuma kira ga sanatan da ya nemi wata kujerar a zabuka masu zuwa, kujera wadda ta fi tasa a yanzu.
The post ‘YAN KABILAR IBO MU HAKURA MU SO JUNA-INJI SANATAN YANKIN IBO UZODINMA appeared first on MUJALLARMU.
Shugaban kungiyar ‘Oodua Peoples’ Congress (OPC)’ Dakta Frederick Fasheun, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke fafutikar a raba kasar da su jira sai shekarar 2114.
Fasheun ya ce wannan shekara ita ce za ta fi dacewa da ballewar Nijeriya tunda a lokacin ne kasar ta cika Shekaru 200 da kafuwa.
Ya ce har tunda Nijeriya ta iya kaiwa shekaru 100 (2014), toh ya kamata kowa ya yi hakuri a kara yin wasu 100, idan abubuwa sun ki, sai a yi batun rabuwa.
A cewar shi “A tunani na, babu wanda ya isa ya mayar da Nijeriya baya…”
“Da wuya a samu kasar da ba ta fuskantar tashe tashen hankulan da ke da alaka da banbance banbancen kabila. Ba a kan mu aka fara, hasali ma abunda ake tsammani kenan ga kasar da take bunkasa”
Game da shigar sa Jam’iyyar GPN, Fasheun ya ce ya yi haka me saboda jam’iyyar PDP da na APC sun riga sun mutu, wanda kuma ana bukatar wata jam’iyya da za ta shigo tsakani ta raba Nijeriya daga tarwatsewa.
The post TOH FA: MASU SON A RABA NIJERIYA KU JIRA SAI NAN DA SHEKARAR 2114-INJI SHUGABAN OPC appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Wani dan Najeriya ya mayar da martani ga ministan matasa da wasanni kan kalaman da ya furta kan talakawan Najeriya – Mutumin ya jaddada cewa talakawan Najeriya suka zabe gwamnatin nan har ya kai ga samun minista Mai magana ya ya ce talakawa sune gatan gwamnatin shugaba Buhari kuma ya gargadi ministan ya san irin kalaman da zai ke furtawa akansu Naci karo da wata maganar da kayi cewar “Talakawa ne ke haddasa matsaloli a kasar nan”.
Idan har hakan ta tabbata to bazan yi mamakin jin haka daga bakinka ba saboda nasan cewar yanzu likafarka ta ci gaba tunda kayi adabo da talakawar da kake janyowa a jikinka lokacin yakin neman zabe.
Kafun akai ga samuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wacce cikin ikon Allah talakawan da kake aibantawa da cewar sune matsalar kasa suka taru suka kafata har ka samu ofishin da yanzu haka kake tada komada, baka da wani batu a wancan lokaci wanda ya wuce batun inganta rayuwar talaka.
Amma yanzu kuma da yake ka samu abin duniya sai talaka ya zamto matsala gareka. Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, mai rubutun ya ce babu shakka duk mai hankali da hangen abunda ke kai komo a kasar nan yasan cewar talakawan da kake aibantawa ko yanzu sun maka rana tunda sun zabi gwamnatin Shugaba Buhari kuma gwamnatin ta yi maka suturar da baka taba samun irinta ba a rayuwar ka.
Ministan matasa da wasanni solomon dalung Mu talakawa muna da yakinin cewar shugaba Buhari yana iya bakin kokarin shi akan inganta walwalar mu, shi yasa ma hankalin shi bai konta ba bare yayi naman wuya irin wacce take wuyar ka.
Duk wanda yasan minista kafun kafuwar gwamnatin shugaba Buhari kuma yasan minista a yanzu tabbas yasan cewar talakawa sunyiwa minista rana domin kuwa gwamnatin da suka kafa ta wanke minista ya fito tsatsaf a idon duniya.
A lokacin da damuwar talakawa suke sa shugaba ramewa su minista kuwa sai cika suke kamar zasu fashe. Inaso ministan yasan cewar talakawa sune gatan gwamnatin shugaba Buhari kuma yasan irin kalaman da zai ke furtawa akansu.
The post KARANTA KAJI: MARTANIN TALAKAWAN NIJERIYA ZUWA GA MINISTAN WASANNI DALUNG appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
An rahoto cewa shugaban kasa Buhari ya yi burus da ganawa ministoci da mataimakansa da sukayi kokarin ganinsa a Landan – Wasu daga cikin su sun so ya sanya masu hannu a kan wasu takardu amma ya yi watsi da su.
Shugaban kasar ya ce lallai tunda Osinbajo na a matsayin mukaddashin shugaban kasa ne shine keda ikon yin haka.
An rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci wasu mataimakansa da ministoci da ke neman yardar sa a kan wasu takardu, da su hadu da mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. Shugaban kasar wanda ke hutun ganin likita a Landan ya mika mulki ga Osinbajo kafin ya bar kasar kuma tun lokacin yana bin abubuwa yadda ya kamata.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu jami’an gwamnati sun yi tattaki zuwa Landan don samun yardarm shugaban kasa amma ya zuba masu kasa a ido inda ya ce lallai a mika dukkan takardu ga Osinbajo don yarda da sa hannu.
Wata babban majiya na gwamnati ta ce: “Duk da cewan yana samun sauki sosai, shugaban kasar na iya bakin ciki kokarin sa don ganin an tsayar da fadar shugaban kasa guda daya. “Ya ki ganin wasu manyan jami’ai da sukayi tattaki zuwa Landan don ganinsa a maimakon kasancewa a bakin aikinsu.
Ya kuma dawo da fayil da takardun wadanda suka kai Landan. “Shugaban kasar ya ba da umurnin cewa akai dukkanin wasu fayil, takardu da al’amuran dake bukatar hukunci ga mukaddashin shugabna kasa.
Baya son a raba kan gwamnati. Buhari na nan aka tsatsauran ra’ayin sa.” Game da rade-radin cewa ba’a bari Aisha Buhari ta ga shugaban kaar ba a lokacin da ta je Landan, majiyar ta ce ba gaskiya bane, ta ce lallai uwargidan shugaban kasar ta gana da shi.
The post SHUGABA BUHARI YA UMARCI JAMI’AN GWAMNATI DASU GANA DA OSINBAJO appeared first on MUJALLARMU.
Wasu musulmai basu san karatun da ake yi a lokacin sallah gawa ba – Sallah gawa ta kunshi kabbara 4 da sallama daya A karshen sallah gawa ana bukatar yiwa dukkan al’ummar musulmai addu’a
1. Bayan kabbara na farko: karanta Surat al-Fatiha (I) Bismillaahir Rahmaanir Raheem (II) Alhamdu lillaahi Rabbil ‘aalameen (III) Ar-Rahmaanir-Raheem (IV) Maaliki Yawmid-Deen (V) Iyyaaka na’budu wa lyyaaka nasta’een (VI) Ihdinas-Siraatal-Mustaqeem (VII) Siraatal-lazeena an’amta ‘alaihim ghayril- maghdoobi ‘alaihim wa lad-daaalleen
2. Bayan kabbara na biyu: karanta Salat Al-Ibrahimiyya zuwa karshen, ba Salat Fatihi ba Sallah Al-jana’iza (Sallah gawa) Allaahumma salli ‘alaa Muhammadin wa ‘alaa ‘aali Muhammadin, kamaa sallayta ‘alaa ‘Ibraaheema wa ‘alaa ‘aali ‘Ibraaheema, ‘innaka Hameedun Majeed. Allaahumma baarik ‘alaa Muhammadin wa ‘alaa ‘aali Muhammadin, kamaa baarakta ‘alaa ‘Ibraaheema wa ‘alaa ‘aali ‘Ibraaheema, ‘innaka Hameedun Majeed.
3. Bayan kabbara na uku: ka yiwa matattun addu’a, amma bisa yadda Manzon Allah (S.A.W) ya koyar. Daya daga cikinsu shi ne: Allaahum-maghfir lihayyinaa, wa mayyitinaa, wa shaahidinaa, wa ghaa’ibinaa, wa sagheerinaa wa kabeerinaa, wa thakarinaa wa ‘unthaanaa. Allaahumma man ‘ahyaytahu minnaa fa’ahyihi ‘alal-‘Islaami, wa man tawaffaytahu minnaa fatawaffahu ‘alal-‘eemaani, Allaahumma laa tahrimnaa ‘ajrahu wa laa tudhillanaa ba’dahu
4. Sa’an nan a karshe bayan kabbara na hudu: ka yiwa dukkan al’ummar Musulmai addu’a 5. A karshe ka sallame da salama daya zuwa dama
The post KARANTA KAJI: YADDA AKE SALLAR JANA’IZA appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Inyamuran Najeriya sun fitar da ‘Dan takara a zabe mai zuwa Cikin wanda ake nema su tsaya takara har da Patience Jonathan Gwamna Rochas Okorocha yana cikin wannan jerin Wata Kungiya ta Inyamamuran Duniya ta zabi ‘Yan takaran ta a zabe mai zuwa. An yi wannan jawabi ne bayan wani taro a Garin Enugu da ke Kasar Ibo.
Inyamuarai sun tabbatar da cewa babu gudu ba ja da baya a 2019 Dame Patience za ta fito takarar Shugaban kasa? Dandalin Mujallarmu.com na samun labari cewa ‘Yan Kudancin Najeriya sun fito da ‘Yan takara kusan 15 a zabe mai zuwa daga ciki akwai matar tsohon shugaban kasa watau Patience Jonathan.
Inyamurai dai sun ce zabe mai zuwa babu gudu ba ja da baya. Yan Kudancin Najeriya sun fito da ‘Yan takara a zabe mai zuwa Sauran dai wadanda ake sa rai su dare kujerar shugaban kasar sun hada da tsofaffin Gwmanoni Orji Uzor Kalu, Peter Obi, da Gwamna Rochas Okorocha, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da dai sauran su.
Kun ji cewa wani Ministan Buhari da ya fito daga Yankin kasar yace matsalar tattali ya hana Shugaba Buhari cika alkawarin da yayi kafin hawa mulki.
The post KUNJI: MATAR TSOHON SHUGABAN KASA PATIENCE JONATHAN ZATA TSAYA TAKARAR SHUGABAN KASA ZABE MAI ZUWA appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Babban bankin Najeriya yayi magana game da tattalin arzikin Najeriya Tattalin arzikin kasar zai yunkura a barin shekaran nan da ke zuwa CBN ke cewa tattalin Najeriya na kara habaka cikin ‘yan kwanakin nan Wani babban Jami’in CBN ke cewa tattalin arzikin Najeriya zai yunkura Najeriya dai na cikin matsin tattali tun bayan hawan Shugaba
Buhari Abubuwa dai sun fara gyaruwa cikin ‘yan kwanakin nan Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a shekarar nan Mun samu labari daga wani babban Jami’in CBN na kasa cewa tattalin arzikin kasar nan zai zabura a karshen shekarar nan.
Jami’in ya bayyana wannan ne bayan wani taro da aka yi a Jihar Legas, tsadar kaya na kara sauka a kasar kamar yadda harsashe ya nuna Inji babban bankin kasar.
Haka kuma dai ana samun sauki wajen canjin dala a yayin da mu ke magana yanzu. A takaice dai zuwa karshen bana abubuwa za su mike a kasar. Makon jiya kun ji cewa Mukaddashin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya rattaba hannu kan kasafin kudin wannan shekara inda Najeriya ke shirin kashe Tiriliyan 7.44. Daga ciki dai dole kasar ta ci bashi domin cike gibin da za a samu.
The post MADALLA: TSADAR KAYA NA KARA SAUKA A KASUWANNI-Inji Bankin CBN appeared first on MUJALLARMU.
Daga Abba Aliyu Suleiman Koki Kano
Shawarata Akan Malaman Nigeria Game Da Kudin Aikin Hajji 2017, Ya kamata Malaman Nigeria Suyiwa Gwamnatin Tarayya Bayani Akan Rage Kudin Aikin Hajji. Da Yakai Kimanin Naira Miliyan Daya Da Rabi (1,500,000) Musamman A Wajan Tafsirin Al Qur’ani Mai Girma A Watan Ramadan Mai Albarka.
Shawarata Akan Malaman Nigeria Game Da Kudin Aikin Hajji 2017
The post Shawarata Akan Malaman Nigeria Game Da Kudin Aikin Hajji 2017 appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Ali Nuhu yanata shan yabo a idanun duniya. domin wannan shine karo na biyu da Ali Nuhu ya rabawa mabukata kayan abinchi tun kamawar wannan azumin.
Jarumin ya raba gero da shinkafa acikin birnin kano a yankin Dala. Ali Nuhu ya raba wannan kayan masarufine domin kyautatawa masu karamin karfi, wanda Allah bai horewa sukuni ko wadata ba.
Wannan abin alkhairi da Ali Nuhu ya yi ya janyo ma shi samin yabo agurin shugaban hisba na kano Malam Aminu Daura,Kuma Malamin yace ya kamata sauran jarumai suyi koyi da Ali Nuhu kodan samin lada mai yawa. Dandalin Kannywood: Jarumi Ali Nuhu ya aiwatar da abun kirki a cikin azumi
Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa Ba wai Ali Nuhu bane kawai ya yi irin wannan sadaka ga marasa wadata. Sani Danja, Mansura Isah, Adam A Zango duk sunyi rabon kayan abinchi ga masu karamin karfi a wannan watan.
Malam Ayuba Dala yana daga cikin wanda ya sami buhun gero dana shinkafa wanda jarumi Ali Nuhu ya raba. kuma ya nuna farin cikinsa afili, sannan ya yi godiya amadadin sauran. Muna fatan Allah ya sakawa Ali Nuhu da alkhairi ameen.
The post DANDALIN KANNYWOOD: JARUMI ALI NUHU YAYI ABIN AZO A GANI ACIKIN AZUMI appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Gwamnatin jihar Taraba ta kafa dokar hana fita a yankin Mambila da Nguroje da ke karamar hukumar Sardauna Rahotanni na cewa wani dan siyasa a yankin ne yaje ya tunzura wasu matasa don tada zauna tsaye.
An kafa dokar hana fita a wasu yankunan da lamarin ya auku baya ga tura karin jami’an tsaro da suka hada da sojoji Wannan sabon tashin hankali ya auku ne biyo bayan yunkurin da wasu matasan kabilar Mambila suka yi na hana jami’an tsaron farin kaya cafke wasu da ake zargin suna da hannu a tashe tashen hankula dake aukuwa a yankin.
Kamar yadda Dandalin Mujallarmu.com ke da labari, rahotanni na cewa wani dan siyasa a yankin ne yaje ya tunzura wasu matasa dake kusa da Nguroje don su hana kamun, kuma ganin basu samu sa’a ba, sai kawai suka shiga fashe fashe da kona taya har zuwa Gembu dake zama hedikwatar karamar hukumar Sardaunan.
Koda yake hukumomin tsaro basu tabbatar da batun asarar rayuka ba, wasu mazauna yankin da rikicin ya rutsa dasu sun bayyana cewa an kona gidaje baya ga rayukan da aka rasa ciki harda na dabbobi. Jami’an tsaro a karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba.
Wasu mazauna yankin da rikicin ya ratsu dasu, sun bayyana hali da ake ciki da kuma iri hasarar da aka yi. Inji wani mazaunan yankin: “Mutane a Mambila ne da Ngurori mutane sun yi ta gudu sai kuma wasu su ka zo domin su kwashe kayan su, aka yi ta kona gidan mutane.
Shi kuma daya mutumin cewa yayi gaskiya a yankin mu abin ba kyau, wallahi ana kone gidajen mutane kuma an kashe wasu.’’ Tuni aka kafa dokar hana fita a wasu yankunan da lamarin ya auku baya ga tura karin jami’an tsaro da suka hada da sojoji kamar yadda ASP David Misal, kakakin rundunan yan sandan jihar Taraban ya tabbatar.
The post LABARI DA DUMI DUMI: GWAMNATIN JIHAR TARABA TA KAFA DOKAR TA BACE A HUKUMAR SARDAUNA appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Bayan barazana da akayi ma ‘yan kabilar Igbo a yankin arewacin Najeriya, wasu Hausawa sun nuna akasin haka don nuna kauna da hadin kai mai dorewa. Sababbin hotuna da suka billo wanda suka shahara a yanar gizo, na nuna wasu Hausawa sanye da kaya irin na al’addun yan Igbo, duk a kokarin sun a nuna cewa sunyi ammana da mutane daga yankin Kudu maso gabas dama sauran yankuna na Najeriya.
A kasa ga hotunan Hausawan dake sanye da shiga irin na al’addun ‘yan Igbo, wanda idan kuka gani zaku dauka cewa ana wani bikin al’ada ne na ‘yan Igbo a Arewa.
Hausawa sanye da kaya irin na al’addun yan Igbo Najeriya daya! Hausawa sunyi shiga irin ta ‘yan kabilar Igbo don nuna kauna, bayan barazanar Arewa Najeriya daya! Hausawa sunyi shiga irin ta ‘yan kabilar Igbo don nuna kauna, bayan barazanar Arewa A wani al’amari makamancin wannan, Dandalin Mujallarmu.com ta rahoto a bayan cewa mukafddashin shugabna kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin tarayyan Najeriya bazata yarda wasu mutane ko kunya sun dunga furta zantukar da zai tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umman kasar ba.
Ya furta hakan ne a ganawa da ya yi da shugabannin kungiyar Arewa sakamakon rikici da ya kunno kai bayan wasu kungiyoyin matsan Arewa sun ba ‘yan kabilar Igbo mazauna yankin Arewa wa’adin watanni uku su bar yankin.
The post ABIN SHA’AWA: KALLI YADDA WASU HAUSAWA YAN ‘AREWA SUKAYI SHIGAR KABILAR IBO DOMIN NUNA KAUNA GARE SU appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Wani bawan Allah mai suna Ajumoti Ajibola ya garzaya kotu a juma’ar da ta gabata yana mai rokon kotu ta raba auren sa da matar sa saboda bata iya girka komai ba.
Mijin ya ce matar tasa mai suna Bolaji bata jin magana kuma bata jin shawara kwata kwata sannan kuma bata iya girki ba. Wani bawan Allah mai suna Ajumoti Ajibola ya garzaya kotu a juma’ar da ta gabata yana mai rokon kotu ta raba auren sa da matar sa saboda bata iya girka komai ba.
Mijin ya ce matar tasa mai suna Bolaji bata jin magana kuma bata jin shawara kwata-kwata sannan kuma bata iya girki ba. Wani ya nemi a raba auren sa da matar sa saboda bata iya girki mai dadi ba Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin yace: “Kwata-kwata bata girmama ni kuma idan nayi mata gyara bata dauka.
Haka zalika uwar ta da ya kamata ta rika gyara mata kullum goyon bayan ta take yi.” “Kuma har ila yau matar tawa bata iya girki mai dadi ba don haka yanzu ina so kotu ta raba auren mu don kuwa na gaji da zarya gidan cin abinci.
” Mijin ya ce. A nata bangaren wadda ake karar ta kalubalanci hurumin kotun ne wajen ikon ta na raba auren inda tace sai babbar kotu ce kadai zata iya yin hakan.
The post ZAUREN MA’AURATA: WANI MIJI YA NEMI A RABA AUREN SA DA MATAR SA SABODA RASHIN IYA GIRKI MAI DADI appeared first on MUJALLARMU.
A wani sako da ya wallafa da harshen Turanci a shafin sa na Facebook a jiya Lahadi, Shehu Sani ya bayyana abubuwa 10 kamar haka:
1. Ta’allaka ga hanya guda daya kacal ta samun kudin shigar gwamnati daga wani sashe na kasar, wanda ke sa su kalli kansu a matsayin saniyar tatsa daga sauran sassan kasar.
2. Mantawa da bala’in da yaki da barkewar daga kasar ya haifar
3. Yadda ‘yan siyasa ke amfani da banbance banbancen addini da kabila wajen juya ‘yan Nijeriya.
4. Yadda kishin kasa ke mutuwa a zukatan ‘yan Nijeriya, kamar yadda ake gani a halin ko in kula da ‘yan Nijeriya ke nunawa a ranar 1 ga watan Oktoba, ranar zagayowar samun ‘yancin kai.
5. Ci gaba da samun gwamnatocin da suka gaza, tabarbarewar tattalin arziki, da karuwar tazarar samu da ke tsakanin masu hannu da shuni da marasa galihu
6. Tasowar ‘yayan zamani masu zafin kai wadanda basu damu da sanin tarihi ba.
7. Ci gaba da amfani da al’adar siyasa wacce ta mayar da hankali ga yadda kowa zai samu kaso daga bitalmalin gwamnati, maimakon mayarda hankali akan yadda kowa zai bayarda nashi gudunmawa wajen ingantashi.
8. Banzatar da hukumomin da aka kafa domin inganta hadin kan ‘yan kasa kamar su NYSC, makarantun gwamnatocin tarayya da sauran su.
9. Son zuciya da tunani mara madafa na wasu kabilu da ke mafarkin raba Nijeriya filla filla ta yadda kowace kabila za ta samu nata kasar.
10. Tsarin tattalin arzikin da ya sanya masu kudi kadan suka danne marasa shi da yawa.
The post KARANTA KAJI: DALILAI 10 DAKE KAWO RARRABUWAR KAWUNAN ‘YAN NIJERIYA-Shehu Sani appeared first on MUJALLARMU.
A cikin kwanaki 5 kacal da fara yin rajistar shirin samar da ayyukan yi na N-Power, mutane 753,307 ne suka yi rajista.
Wannan adadi dai ya ninka na mutanen da suka yi rajista a shekarar 2016.
Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman akan harkokin samar da ayyukan yi, Afolabi Imoukhuede shi ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN a jiya Lahadi a Asaba, babban birnin jahar Delta.
Ya ce a cikin kwanaki 5 kacal, an ninka adadin da aka samu a 2016, duk da cewa an shafe watanni 2 da rabi ana yin rajista a wancan lokacin.
Imokhuedu ya bayyana cewa bangaren koyarwa na shirin shi ya fi kawo mutane da rajistoci 470,456, yayin da shirin noma ya samu 127,315.
Bangaren kiwon lafiya ya kawo mutane 85,691, yayin da a sabon bangaren karbar haraji aka samu mutane 69,842.
A cewar mai bada shawarar, shirin ya samu wannan nasara ne saboda mutane yanzu sun gasgata shirin, sabanin a shekarar da ta gabata.
Sai dai ya ce duk da yawan mutanen da aka samu, gwamnati ba za ta iya daukar fiye da dubu 300 ba, gudun kar a kere kasafin kudin da aka warewa shirin a wannan lokaci.
The post KWANAKI 5 KACAL MUTANE 753,307 SUKAYI RIJISTA A SHIRIN DAKE BUKATAR MUTANE 300,00O-N-POWER appeared first on MUJALLARMU.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Ana shirin kawo wasu sauye-sauye a wasan kwallon kafa ciki har da rage lokacin wasan ya zama minti 60, inda za a rika tafiya hutu bayan minti 30. – Majalisar da ke dokokin wasan ta duniya (ifab) ta ce tana son kawo wannan sauyi ne saboda kusan minti 60 kawai ake yi na tsagwaron wasa a cikin minti 90, sauran lokacin duk kusan dabaru ne na bata lokaci da ‘yan wasa kan yi.
Wani sauyin da ake shirin kawowa kuma shi ne, a duk lokacin da dan wasa ya buga fanareti ba ta shiga ba ta dawo, babu damar a sake bugawa, an yi asararta. Sauran shawarwarin su ne hada agogon filin wasan ya zama yana aiki daidai da agogon alkalin wasa, sannan da wata sabuwar doka da za ta ba dan wasa dama ya ba wa kansa da kansa kwallo a lokacin da zai yi bugun tazara.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa tsohon dan wasan Chelsea na gaba Gianfranco Zola yana goyon bayan rage lokacin wasan daga minti 90 zuwa 60, saboda ya ce yana ganin akwai kungiyoyi da dama da ke bata lokaci su ki tsayawa su yi wasa idan suna kan gaba.
Shi ma mai tsaron ragar Arsenal Petr Cech ya goyi da bayan Zola inda ya bayyana cewa a yanzu kusan minti 25 ne kawai ake yi a kowane kashi daya na wasan, saboda haka idan aka rage lokacin za a riga ganin tsagwaron wasa ne kawai.
Ifab ta kunshi hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, da hukumomin kwallon kafa na yankuna hudu na Birtaniya – Ingila da Scotland da Wales da Ireland ta Arewa.
The post LABARI DA DUMI DUMIN: KUNGIYAR KWALLON KAFA TA DUNIYA FIFA ZATA RAGE MINTU NAN WASANNI DAGA MINTI 90 ZUWA MINTI 60 KACAL appeared first on MUJALLARMU.