CBN za ta rika saidawa ‘yan canji Dala domin a samu sauki
Babban bankin kasar na CBN ya kawo wani sabon tsari da zai sa Dala ta kara araha a kasar.
Darajar Naira na ta kara sama tun daga kusan N500 har zuwa N360 a cikin wannan watan CBN za ta rika saidawa ‘yan canji Dala domin a samu sauki CBN na kasar ya kawo sabon tsari Rahotannin da ke zuwa ga

Mujallarmu.com sun nuna cewa farashin Dala zai kara yin sauki a dalilin wani tsari da CBN za ta fara kwanan nan. CBN din za ta rika sayar da Dala ga ‘yan canji domin a samu sauki a kasar.
Bankin kasar na CBN zai rika saida Dala sau biyu a kowane mako ga ‘yan canji domin a samu yalwar kudin a ko ina. Babban Jami’in Bankin Isaac Okorafor ya bayyana haka a Abuja a Jiya Alhamis.
CBN za ta rika saidawa ‘yan canji Dala domin a samu sauki CBN za ta rika saidawa ‘yan canji Dala CBN za ta kara kudin da ake ba ‘yan canjin zuwa Dala 10,000 a kowane karo Inji Mista Okorafor.
Za a fara wannan tsari ne daga Ranar Litinin dinnan mai zuwa Inji CBN. Hakan dai zai kawo yalwar Daloli a kasar kuma farashin ya kara karyewa.
Jiya Naira ta sha kasa a kasuwar Duniya inda ta yi kasa a kan Dala daga kan N382 zuwa N385. Dalar Pounds ta Ingila kuwa dai ta kai N400 yanzu a kasuwar ‘yan canjin a dalilin mugun neman Dalar da ake yi.
The post BABBAN BANKIN NIJERIYA CBN ZAI RINKA SAIDAWA YAN CANJI DALA DOMIN A SAMU SAUKI appeared first on MUJALLARMU.