Shugaban kasa ya dauki mataki; Majalisa ta hana
Majalisar Wakilai sun takawa shugaban kasa Muhammadu Buhari burki inda suka ce abin da yayi ya saba dokar tsarin mulki na kasa Shugaban kasa ya dauki mataki; Majalisa ta hana Majalisa tace wa Shugaban kasa bai isa ba Kwanaki ne dai

Mujallarmu.com ta rahoto cewa shugaban kasa Buhari ya karawa wata Sakatare ta din-din-din wa’adi bayan shekarun ta na aiki sun zarce.
Majalisa ta tabbatar da cewa dole wannan Sakatariya ta ajiye aiki ba da wata-wata ba. Majalisar Wakilai tace dole Jamila Shu’ura da shugaba Buhari ya karawa wa’adi ta tattara ina-ta-ina-ta ta bar ofis.
Majalisar tace babu inda dokar tsarin mulki na kasa ta ba shugaban kasa damar ya kara wa’adin ma’aikacin Gwamnati bayan ya zarce shekarun aiki.
Shugaban kasa ya dauki mataki; Majalisa ta hana Shugaba Buhari ya dauki mataki Majalisa ta kafe Majalisar dai dama ta gargadi shugaban kasar inda ta ke ja masa kunne da ya guji dabbaka hannu a kudirin da zai kafa Hukumar Peace Corps a matsayin Jami’an tsaro na kasa. Tun a bara dai Hajiya Jamila ta cika shekarun aiki inda Majalisa tace dole ta tattara ta bar ofis.
Jiya kuma Majalisar Dattawa ta kawo garambawul da dama a harkar zabe daga cikin an tsaida kudin fom din takarar shugaban kasa a kan kudi Naira Miliyan 10. Majalisar ta kuma ragewa Gwamnoni karfi wajen zaben masu fitar da gwani a zaben farko.
The post MAJALISAR DATTAWA NA KOKARIN TAKAWA SHUGABA BUHARI BURKI AKAN WANI MATAKI DAYA DAUKA appeared first on MUJALLARMU.