Kone-konen Boko Haram sun jawo fari da yunwa a Borno
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Yan Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a jihar Borno – Kone konen da kungiyar Boko Haram ta dinga yi a jihar Borno sun sa jihar ta shiga wani halin yunwa da talauci.
Yawancin sassan jihar Borno sun yi shekaru hudu ko fiye babu damar yin noma sanadiyar rashin tsaro, sace sace da kashe kashen mutane da kungiyar ke yawan yi Kone konen da kungiyar Boko Haram ta dinga yi a jihar Borno sun sa jihar ta shiga wani halin fari na yunwa saboda baicin karuwar kwararowar hamada yawancin jama’ar jihar basu iya fita zuwa noma ba.
Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya wadda ta kasance mahaifar kungiyar Boko Haram ta kwashe fiye da shekaru biyar tana cikin mugun azabar kungiyar ta’addancin.
A duk cikin jihohin arewa maso gabas jihar Borno ce ta fi fama da hare-hare da kone konen da ‘yan Boko Haram suka haddasa. Kone-konen Boko Haram sun jawo fari da yunwa a Borno Kone-konen Boko Haram sun jawo fari da yunwa a Borno Bayan sun kwace garuruwa da dama sun kashe dubban mutane, sun lalata muhallai sai kuma suka shiga kone kone. Hatta sansanonin da aka samar ma wasu masu gudun hijira lokacin da rikicin ya fara basu tsira ba.
Yawancin sassan jihar Borno sun yi shekaru hudu ko fiye babu damar yin noma sanadiyar rashin tsaro, sace sace da kashe kashen mutane da kungiyar ke yawan yi. Sau tari dan abincin da ya rage a wasu wuraren kungiyar na bi tana sacewa kana ta kone kauyukan bayan ta kashe na kashewa ko kuma wasu sun samu sun arce. Kungiyar ta sa jihar dake kusa da hamada fadawa cikin wani halin kunci.
A baya Mujallarmu.com ta ruwaito inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke cewa Najeriya na iya fuskantar rikicin jama’a idan ba’a kula da mutane miliyan biyu da yan Boko Haram suka mamaye gurin su ba.
Ya bayyana hakan ne a gurin wani taro da shugaban kungiyar Tijjaniya, Sheikh Sharif Ibn Mohammad, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
The post HARE HAREN BOKO HARAM KA IYA JANYO MATSANANCIYAR YUNWA DA TALAUCI A JIHAR BORNO- appeared first on MUJALLARMU.