Ikon Allah: Yadda wata yarinya ta haifi ‘yan 4 su ka kuma koma
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Matar Gwamnan Jihar Bauchi ta dauki nauyin kula da ita Sai dai yanzu kuma wadannan yara sun komawa ubangijin su.
Mujallarmu.com ta samu labarin cewa wata yarinya a Jihar Bauchi mai suna Huzaifatu ta haifi yara ‘yan hudu a Garin Azare dake Karamar Hukumar Katagum.
Wannan abu ya faru ne mako biyu da suka wuce. Hajiya Hadiza Abubakar matar Gwamnan Jihar Barista M. A Abubakar tayi wuf ta garzaya Garin tare da Kantomar Yankin domin duba lafiyar wannan yarinya da iyalin ta.
Nan take matar mai girma Gwamna ta dauki nauyin kudin asibiti.
Sai dai kuma kash! An yi rashin ‘ya ‘ya 3 daga cikin ‘ya ‘ya 4 da aka haifa. Hajiya Hadiza Uwargidar Gwamna tayi ta’aziyya ga dangin wannan karamar yarinya mai-jego Huzaifatu a Garin Azare.
The post WATA KARAMAR YARINYA MAI SUNA HUZAIFATU TA HAIFI ‘YAN HUDU A GARIN AZARE JIHAR BAUCHI appeared first on MUJALLARMU.