Ma’aikata sun jefi gwamnan jihar Kogi akan rashin biyan albashi
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya sha da kyar a hannun mutanensa – Ma’aikata sun yi ma gwamnan ihu ‘a biya mu kudin mu’ Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya sha da kyar a ranar Laraba 12 ga watan Afrilu a hannun ma’aikatan jihar yayin daya kai ziyarar aiki garin Idah.
Majiyar Dandalin Mujallarmu.com ta shaida mana cewar gwamnan yaje garin Idah ne da nufin kaddamar da fara aikin hanya, bayan matasan garin sun hangi wucewar gwamnan ne sai suka fara dakon dawowarsa, dawowarsa ke da wuya, sai suka tare hanyar.
Jami’an tsaron dake gadin gwamnan sun yi kokarin tarwatsa matasan, amma abin yaci tura, sai wasu daga cikin matasan yan kasada suka fara jifar motar gwamnan da duwatsu suna kiran “Ka biya ma’aikata albashinsu” Ma’aikata sun jefi gwamnan jihar Kogi akan rashin biyan albashi Yahaya Bello A wani kaulin kuma, daya daga cikin abinda gwamnan zai yi ya hada da rushe gidansu wani kasurgumin dan fashi a garin Idah, amma sakamakon lamarin daya faru na jifa, nan da nan ya tattara ya koma fadar gwamnati.
Sai dai tun bayan faruwar lamarin, jama’a sun tsere daga garin Idah don gudun kawo musu farmaki daga jami’an tsaro, ita ma gwamnatin jihar ba tayi tsokaci ba dangane da faruwar lamarin.
The post GWAMNAN JIHAR KOGI YASHA DA KYAR BAYAN RUWAN DUWATSU A HANNUN MA’AIKATA AKAN RASHIN BIYAN ALBASHI appeared first on MUJALLARMU.