Tsoron jifa ya fara hana Sanatocin Arewa zuwa mazabun su
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Al’ummar jihar Bauchi, sun bayyana cewa tsoron jifa ya hana Sanatocin su zuwa Bauchi tun bayan jifan da akayiwa sanata Ali wakili da sanata Isah Hamma Misau.
Sanatocin wadanda su ka ci zabe, a karkashin jam’iyyar APC,amma daga bisani suka yi butulci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Barista Muhammad Abdullahi Abubakar.
Gami da watsi ga talakawan jihar Saboda wasu bukatunsu wanda bana talakawan jahar ta Bauchi ba. “A dalilin haka yanzu sanatocin suka, shirya wata makarkashiya domin kawo rudani a fadin jihar. Wanda ta haka su ke son samun damar shiga cikin jihar ta Bauchi domin gujewa fushin talakawa.
Yanzu haka dai sun dauki hayar wasu matasa su kimanin 200 domin jifan mai girma gwamnan Barista Muhammad Abdullahi Abubakar” a wajen taro kamar yadda wani matashi wanda ya nemi a sakaya sunansa kuma yana cikin wandanda aka bawa wannan kwangilar ya bayyana.
Dandalin Mujallarmu.com ta tattaro cewar Dama dai an dade ana zargin sanatocin jihar ta Bauchi da yunkurin kawo rikici a fadin jihar, da kuma kauda hankalin mutane daga ayyukan Alkhairi da mai girma gwamnan M.A Abubakar ya ke yi a fadin jihar.
The post TSORON JIFA YA HANA SANATOCIN AREWA ZUWA BAZABUN SU appeared first on MUJALLARMU.