Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

LABARI DA DUMI DUMI:SHUGABA BUHARI YA SALLAMI SAKATAREN GWAMNATI BABACHIR LAWAN

$
0
0

Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA 

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shugaban kasa ya dakatar da sakataren gwamnatin Babachir daga aiki – Bugu da kari shugaba Buhari ya dakatar da shugaban hukumar tsaron sirri na NIA, Oke Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a gudanar da bincike cikin badakalar bada kwanagilolin ayyukan jin kai a yankin Arewa maso gabas da ake tuhumar sakataren gwamnati Babachir David Lawal da shi.
Haka zalika shugaban ya sallami sakataren nasa har sai an kammala gudanar da bincikensa. Bugu da kari shugaba Buhari ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike kan makudan kudaden da aka bankado a wani katafren gida dake jihar Legas, wanda hukumar tsaron sirri ta NIA tayi ikirarin cewa nata ne.
Binciken da Buhari ya bada umarnin a gudanar ya hada da gano yadda NIA ta mallaki wadannan makudan kudade, ta yaya, way a basu da kuma umarnin waye ya basu kudin, sa’annan shugaba Buhari ya bukaci a gano an karya doka a hakan ko kuwa? Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA Babachir David Lawal Shima a nan Dandalin Mujallarmu.com ta ruwaito Buhari ya bada umarnin dakatar da shugaban NIA, Ambassador Ayo Oke, har sai yadda halin binciken ya nuna.
Buhari ya dakatar da sakataren gwamnati da shugaban hukumar tsaron sirri, NIA Shugaban hukumar tsaron sirri, NIA, Jakada Oke Saboda haka shugaban Buhari ya kaddamar da kwamitin mutum uku data kunshi Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, mashawarcin shugaban kasa a bangaren tsaro, Munguno da kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo a matsayin shugaban kwmatin.
Shugaba Buhari ya ba kwamitin sati biyu su karkare bincikensu tare da mika masa rahoto cikin sati 2, don haka ya umarci babban jami’i na biyu a ofishin sakataren gwamnati da na hukumar NIA dasu dauki ragamar mulki har sai an kammala bincike.

The post LABARI DA DUMI DUMI:SHUGABA BUHARI YA SALLAMI SAKATAREN GWAMNATI BABACHIR LAWAN appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>