Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Shugaba Muhammadu Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau Laraba, 19 ga watan Afrilu babu wanda aka gani daga cikin mukarraban gwamnati da aka ga ya halarci dakin da ake gudanar da taron.
Fadar shugaban kasa bat ace komai ba akan batun a lokacin wannan rahoton Ba’a gudanar da Taron majalisar zartarwa da aka saba gudanarwa a duk mako ba a yau. Har zuwa karfe 12 saura na safiyar yau, babu wanda aka gani daga cikin mukarraban gwamnati da aka ga ya halarci dakin da ake gudanar da taron.
Kuma har zuwa lokacin wannan rahoton babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa kan dalilin kin gudanar da taron. Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau Buhari ya soke taron majalisar zartarwa na yau
Idan ba a mance ba a baya Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa sakamakon rashin halartar taron da shugaba Buhari bai yi ba a zaman da aka yi a makon da ya gabata, ya jawo yada jita-jitar cewa shugaban na fama da rashin lafiya, har sai da ta kai ga ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya fito ya karyata batun, inda ya ce shugaban na nan cikin koshin lafiya.
Lai Mohammed ya kara da cewa rashin halartar shugaban kasar ofis ba wai yana nufin ba ya aiki bane.
The post SHUGABA BUHARI YA SOKE TARON MAJALISAR ZARTARWA A KARO NA BIYU appeared first on MUJALLARMU.