Dariya Zalla: BAKATSINE DA BANUPE
Marubuci:HarunaSp Dansadau

Wani Bakatsine da wani Banupe ne su ka yi laifi, sai a ka kai su kotu. Ga yadda zaman kotun ya kasance.
Alkali:- Sakamakon ina cikin farin ciki da haihuwar mata ta lafiya, zan yi mu ku rangwame. Kowa ya fadi
iyakance yawan bulalan da ya ke so a yi ma shi, da kuma yadda ya ke so ayi masa bulalan.
Banupe:- Toh, ranka ya dade, ina so a yi min bulala goma, amma a dora filo guda goma ajiki na, kafin a
fara bulalan!
Alkali:- Babu laifi, ku yi masa yanda ya ce. Aka yi wa Banupe bulala 10, ba tare da ya ji zafi ba.
Alkali:- Bakatsine?.
Bakatsine:- Ranka ya dade, ina son a yi min bulala (100), amma a dora wannan Banupen a baya na, kafin
a fara bulalan!
Alkali:- Babu laifi. Ku dora shi a bayan sa, a yi masa bulalan!! A ka yiwa Banupe bulala (100) a matsayin
Bakatsine…!
The post MUSHA DARIYA ZALLAH:BAKATSINE DA BANUPE appeared first on MUJALLARMU.