Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

MASU CEWA SHUGABA BUHARI YAYI MURABUS SUNA DA TABIN HANKALI:Inji Doyin Okupe

$
0
0

Cewa Buhari yayi murabis rashin hankali ne – Doyin Okupe

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Mai magana da yawiun tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, yayi c akan masu kira ga Buhari yayi murabus -yace gaskiya da adalci ne kawai zai hada kanmu da lafiya da kasa Abin kunya ne da rashin hankali yadda wasu yan Najeriya ke gunaguni kan rashin lafiyan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon mai Magana da yawun shugaban Goodluck Jonathan, Doyin Okupe ne yayi wannan Magana a wata jawabi da yayi ranan Juma’a. Yace: ” Rashin lafiya ba abinda zaka tuhumce mai shi bane.
Babba da yaro na rashin lafiya kuma su mutu. Mutuwa ba na tsoho bane ko karami, talaka ko maikudi,”.
Okupe Yace yan siyasa su sani cewa tun lokacin da aka dawo mulkin demokradiyya 1999 shekaru 18 da suka gabata, kudancin Najeriya ne sukayi mulki na kusan shekaru 14, arewa shekara 4 kawai tayi.
Irin wannan rabe-raben siyasan ba sabon abu bane a siyasanmu. A shekarar 1998, saboda rashin adalcin da mukayi tunanin an yiwa ya arewa maso yamma, an amince da basu shugabancin kasan.
” Ba bisa kundin tsarin mulki bane amma kuma bai sabawa doka ba. Abune mai kyau a siyaance kuma ya hada kanmu gaba daya.” ” Wajibi ne mu daina amfani da mutuwa wajen yaudaran kanmu a siyasance da gwamnatacce.
Gaskiya, soyayya, adalci da daidaito ne kawai yai kawo cigabanmu da zaman lafiya. “

The post MASU CEWA SHUGABA BUHARI YAYI MURABUS SUNA DA TABIN HANKALI:Inji Doyin Okupe appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>