Kalmomin yorubanci 10 masu alaka da Larabci
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Kalmomin yorubanci masu alaka da harshen larabci akwai kalmomin yorubancin da dama da ake amfani da su wanda aka samu daga kalmar larabci Harshen yorubanci wanda ke dauke da rinjayi harshen larabci kuma akwai da yawa daga kalmomin da muke amfani da kowace rana wanda yana da alaka da yorubanci.

Dandalin Mujallarmu.com ta tattaro wasu kalmomin yorubanci masu alaka da harshen larabci mai yiwuwa ba a sani ba.
1. Wahala ‘Wahala’ na nufin matsala a yorubance, an samu daga kalmar larabci “wahla,” wanda yake nufin “tsoro,” ko “ta’addanci.”
2. Iwaju ‘Iwaju’ na nufin gaba a yorubance, an samu kalmar ne daga Larabci “al-wajh,” wanda yake nufin “gaba” ko “fuska.”
3. Faari ‘Faari’ na nufin takama a yorubance, an samu kalmar ne daga Larabci “Fakhr,” wanda yake nufin “girma” ko “girman kai”.
4. Barika ‘Barika’ na nufin taya murna a yorubance, an samu kalmar ne daga Larabci “al-Baraka,” wanda yake nufin “gaisuwa.” Ko “albarka”
5. Asiri ‘Asiri’ na nufin asirce a yorubance, an samu kalmar ne daga larabci “as-sirr” inda shi ma yana nufin asiri
6. Ara ‘Ara’ yana nufin tsawa a yorubance, an samu daga kalmar larabci “ar-ra’d.
The post KARANTA KAJI:KALMOMIN YARABANCI GUDA GOMA MASU ALAKA DA LARABCI appeared first on MUJALLARMU.