Hadari: Jami’an tsaro sun kashe wani Minista
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Jami’an tsaro sun budawa wani Ministan kasar Somalia wuta da kure yanzu haka an birne wannan Minista Abdullahi Sheikh cikin takaici Shugaban kasar ya bada damar ayi bincike game da kisan Ministan kasar Somalia ya bar Duniya bayan da Jami’ai su ka harbe sa.
Wannan abun dai ya faru ne bisa kuskure,Shugaban kasa ya bada umarni ayi bincike. Jami’an tsaro sun budewa wani Minista wuta bayan da su kayi tsammanin wani Tsagera ne.
Yanzu dai Minista Abdullahi Sheikh Abbas mai shekaru 31 yayi ban–kwana da Duniyar.
Shugaban kasar Somalia Muhammad Sheikh ya bada umarni ayi bincike game da kisan da aka ce ba da sani aka yi ba.
Shugaban kasar yace rasuwar Ministan na sa abin takaici ne kwarai da gaske.
The post JAMI’AN TSARO SUN KASHE WANI MINISTA ABISA KUSKURE appeared first on MUJALLARMU.