Babu wanda zai iya tilasta Buhari sauka daga mulki
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Kungiyoyin tabbatar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya tace babu wanda zai iya tilasta Buhari sauka daga mulki kungiyar ta ce kiran da ake yiwa shugaba Buhari da ya yi murabus janyewar hankali ne kawai Kungiyoyin tabbatar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya ta ce babu wanda zai iya tilastawa shugaban kasar Muhammadu Buhari sauka daga mulki.
A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu, kungiyar ta ce tun da shugaban bai gayawa wani cewa ba zai iya mulkin ba, ba wanda zai iya tilasta shi ya sauka.
Kungiyar ta bayyana cewa kiran da ake wa shugaba Buhari cewa ya dauki hutu kan kiwon lafiyarsa don ganin likita a Landon, wannan wata yunkurin juyin mulkin farar hula ne.
Kamar yadda Dandalin Mujallarmu.com ke da labari , kungiyar ta ce kiran da ake yiwa shugaban kasar da ya yi murabus janyewar hankali ne kawai.
Hadaddiyar kungiyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi wa shugan kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun lafiya.
The post BABU WANDA ZAI IYA TILASTAWA SHUGABA BUHARI SAUKA DAGA KAN MULKI appeared first on MUJALLARMU.