A Yau Za a Mika Wa Buhari ‘Yan Matan Chibok 82 Da Aka Kara Cetowa
Marubuci:Haruna Sp Dansadau

A yau Lahadi, 7 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin ‘yan matan Chibok 82 da aka ceto a jiya.
An ceto’ yan matan ne bayan da aka yi musayar su da wasu firsunonin Boko Haram da gwamnati ke rike da su.
Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa da nai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya fitar a daren jiya Asabar.
Yanzu haka adadin ‘yan matan da gwamnati ta ceto ya haura dari, idan aka hada da 21 da aka ceto a baya.
Sama da shekaru 3 kenan tunda mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata fiye da 200 a makarantar sakandiren Chibok da ke jahar Borno.
Garba Shehu ya bayyana cewa jami’an tsaron Nijeriya sun shafe watanni suna yarjejeniya da mayakan kafin a cimma wannan nasara.
Ya ce shugaba Buhari ya na mika godiyar sa garesu da gwamnatin Switzerland, kungiyar Red Cross, da kungiyoyi masu zaman kansu na gida da na waje.
The post A YAU NI AKA MIKA WA SHUGABA BUHARI ‘YAN MATAN CHIBOK 82 DA AKA KARA CETOWA appeared first on MUJALLARMU.