Kyakyawan Ladduban Du’a’i Guda Goma Shabiyar
Marubuci:Haruna Sp Dansadau

1-Yin Imani da kuma yarda Allah yana amsa kiran bawansa kuma ya biya masa
buqatarsa,da kuma yiwa Allah biyayya da bari saba masa.
@Suratul Baqara-186.
2-Yin Ikhlasy,wato kada ka roki kowa sai Allah shi kadai a lokacin adduarka da kuma
sauran ibadu gaba daya.
@Suratul Bayyinah-5
3-Yin rokon Allah da Sunayansa madaukaka.
@Suratul A’araf
4-Ka fara da yabon Allah da girmama shi da yiwa Allah kirari,sannan karoki abinda kake buqata.
@Albany ya Ingantashi
5-Sannan yin salati ga Annabi s.a.w domin duk adduar da babu salatin Annabi s.a.w acikinta,ba’a bude mata kofofin sama.
@Dhabarany Albany ya Ingantashi.
6-Fuskantar alqibla a lokacin yin adduar.
@Muslim
7-Daga hannuwa a lokacin yin addua.
@ Albany ya Ingantashi.
8-Ka roki Allah da cikin hannunsa,Ma’ana ya bude hannayansa cikinsu yana kallon sama.
@ Albany ya Ingantashi.
9-Ka riqa samun yakini akan Allah yana amsa adduarsa.
@ Albany yace Hadisine Hasan
10-Yawaita rokon Allah a kowane lokaci da rashi yin gaggawa acikin Addua.
@Bukhari da Muslim
11-Halarto da hankali a lokacin addua da yin azama wajan rokon Allah.
@Bukhari da Muslim
12-Yin kwadayi da fargaba da qanqantar da kai ga Allah a lokacin yin Addua.
@Suratul A’araf-55
13-Maimaita addua sau uku a lokacin yinta.
@Bukhari da Muslim
14-Nisanta cin haramu da kokarin yin rayuwa ta halas.
@Muslim
15-Boye sauti a lokacin addua domin addua sirrice tsakanin bawa da Allah.
@Suratul A’araf-55
@ Suratul Maryam-3.
The post KYAWAWAN LADUBBAN DU’A’I GUDA GOMA SHA BIYAR appeared first on MUJALLARMU.