Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KARANTA KAJI: ABUBUWA 3 DA AKE SARAN MUKADDASHIN SHUGABAN KASA ZAI FARA AIKI AKAN SU

$
0
0

         Abubuwa 3 da ake tsammani Osinbajo ya fara da su

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Farfesa Osinbajo ya zama mukaddashin shugaban kasa ana tsammani ya fara wasu ayyuka da ya zaran ya shiga Ofis akwai maganar Sakataren Gwamnati.
   
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma asibiti Fadar shugaban kasar tace babu abin tada hankali domin Osinbajo zai ja ragama Daga cikin abubuwan da zai fara tabawa watakila akwai:
Abubuwa 3 da ake tsammani Osinbajo ya fara da su kamar haka:-
1. Sakataren Gwamnati Farfesa Osinbajo ya jagoranci kwamitin da aka nada domin binciken Babachir Lawal kuma an sa rai a mikawa shugaban kasar rahoto a yau. Watakila mukaddashin shugaban kasar ya dauki mataki game da kujerar da kuma Babachir da aka dakatar.
2. Kasafin kudi Har an shiga watan Mayu amma Majalisa ba ta amince da kasafin kudin shekarar bana ba. Yayin da lokacin ke kurewa ba mamaki mukaddashin shugaban kasar ya gana da shugabannin Majalisa. Abubuwa
3. Sababbin Ministoci Majalisar Dattawa ta tantace Farfesa Ikani Ocheni da Sulaiman Hassan a matsayin Ministocin Najeriya domin maye gurbin Amina J. Mohammed da Marigayi James Ocholi.
Ana sa rai Osinbajo ya zabi ma’aikata ya bayyana ofishin da za su fara aiki.

The post KARANTA KAJI: ABUBUWA 3 DA AKE SARAN MUKADDASHIN SHUGABAN KASA ZAI FARA AIKI AKAN SU appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050