An gurfanar da matan da ta rotsawa tsohon saurayinta kai da karfe
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Zamani ya kawo mace na iya jima namiji rauni shi kuma namiji saboda ragonci ya kai karanta wurin hukuma A yau ne Litinin, 8 ga watan Mayu, aka gurfanar da wata mata mai suna, Debbie Mike, a babban kotun majistaren Ebute Meta a jihar Legas.

An gurfanar da Debbie ne saboda azabar da ta ganama tsohon saurayinta, Lanre Adewole, yayinda suka samu sabani. Sgt. Kehinde Olatunde ya fadawa kotun cewa ta aikata wannan aika-aika ne ranan 5 ga watan Mayu a gida mai lamba 3a, Sadiku St., Sari-Iganmu a Orile jihar Legas.
“An samu sabani ne tsakanin Debbie da Adewole, yaran mai gidan.” “Ta fadawa Adewole cewa kwanon rufintana yoyo amma tsohon masoyin nata yayi banza da ita.”
“Kawai sai suka fara fada, Debbie ta dauki karfe ta bugawa Adewolw a kai, ta ji masa ciwo.” Alkalin kotun majistaren, Mrs Bola Folarin-Williams, ta bada belin Debbie kan N20,000 da kuma shaidan hakan,an dakatad da karan zuwa ranan 11 ga watan Mayu.
The post KALUBALE GA SAMARI: WANI SAURAYI YA MAKA BUDURWAR SA KOTU SABODA TA FASA MASA KAI appeared first on MUJALLARMU.