Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KULA DA LAFIYA JARI: HANYOYIN KARE KAI DAGA CUTAR KOLERA DA ATINI DA TAIFOT GOMA 15

$
0
0

        Hanyoyin Kariya Daga Cutar Kolera Da Atini Da Taifot

               Hanyoyin Kariya Daga Cutar Kolera Da Atini Da Taifot

Cutar Kolera, Atini da Taifot cuta ce da take yaduwa a lokacin damina kuma ana samun su ne a gurbatacen ruwa.

Hanyoyin kariya daga wadanan cuta shine?
1-A guji bayan-gida barkatai a hanya da gefen magudanan ruwa ko rijiya ko kogi kamar dabbobi. A koyi hali irin na kyanwa wadda takan tabbatar ta bizne ba-hayanta.
2-Kada a gina rijiya dab da bayan-gida, a ba da tazarar akalla kafa 50.
3-Gina gidajen ba-haya na zamani a wuraren zaman jama’a kamar kasuwanni zai rage yawan ba haya barkatai, da kusa da magudanan ruwa.
4-Saka dokar-ta-baci ga duk wanda aka samu yana bayan-gida a bainar jama’a ko yana zub da ba-haya irin na gidaje a magudanan ruwa.
5-A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha. Ruwan famfo yana da sinadarin chlorine da kan kashe kwayoyin cutar. Amma wasu lokuta bututun ruwa sukan fashe su sake gurbata da ruwan kwatami ta yadda sinadarin ma ba zai yi tasiri ba.
6-Hukumomin gidan ruwa su tabbata an tace kuma an saka sinadarin chlorine yadda ya kamata kafin a sako ruwa.
7-A guji shan kankara da ba a tabbatar daga ruwan da aka hada ta ba. Idan ya zama dole, a ribanya ledar jikin kankarar kafin a sa a ruwa mai tsabta don ya yi sanyi.
8-A tabbata an wanke hannaye da sabulu bayan an yi bayan-gida ko kuma an yi wa yara tsarki da kuma kafin cin abinci. Yawan wanke hannu da sabulu yana hana kamuwa da wadannan cututtuka kwarai da gaske. Kuma a tabbata an fara yin amfani da wani mayani kamar kara ko toilet paper bayan an yi bayan-gida, daga bisani kuma a sa ruwa.
9-Masu sayar da abinci su guji taba abin sayarwar da hannu, sai da babban cokali ko marar zuba abinci.
10-Duk matar da ba a yarda da tsabtarta ba a kiyayi abincinta.
11-A kiyaye tsabtar muhalli da ta bayan gida don kada kuda da kyankyaso su samu wurin zama.
12-A rufe duk wani abinci da abin sha da aka ci, don kada kuda ko kyankyaso ya hau.
13-Kada a ci kayan lambu irin su latas da karas da ba dafa su ake yi ba, har sai an wanke su a ruwa mai gishiri, an kuma dauraye. Ruwan gishiri yana aiki a nan kamar sabulu.
14-Da zarar an ga alamun gudawa, a samo ruwan gishiri da sukari na sachet wato ORS a hada a fara ba mara lafiya kafin a garzaya asibiti mafi kusa. Idan ba a samu ORS ba a samu gishiri rabin karamin cokali da sukari cikin karamin cokali biyar a hada a ruwa mai tsafta kwatankwacin babban kofi, a bayar a hankali har a kai asibiti.
15-Dole a tafi asibiti domin a duba maras lafiya sosai a ba shi magani ko karin ruwa saboda mara lafiya zai iya amai ya dawo da ruwan gishirin da aka ba shi. Sinadarin ORS ba shi zai tsayar da gudawa ba.

The post KULA DA LAFIYA JARI: HANYOYIN KARE KAI DAGA CUTAR KOLERA DA ATINI DA TAIFOT GOMA 15 appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050