Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

YIWA ADDINI HIDIMA: GWAMNAN JIHAR BAUCHI YAYI BIKIN BUDE WANI BABBAN MASALLACIN JUMA’A DAYA GINA-HOTUNA

$
0
0

An bude babban masallacin juma’an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna).

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya gina wani babban masallaci a Bauchi wanda aka bude a ranar juma’a da ta gabata,Babban masallacin na daya daga cikin manya-manyan masallatai masu tarihi a Jihar Bauchi.

Mazaunan unguwan da aka gina masallacin sunyi fatan alkhairi ma gwamnan kan gina wannan masallaci An budi babban Masallacin juma’an da gwamnan Bauchi ya gina a kofan Galadiman Bauchi a ranar juma’a 26 ga watan Mayu.
Mai girma gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ya bude babban masallacin juma’a daya gina a kofar gidan Galadiman Bauchi, a unguwan jahun da ke cikin garin Bauchi.
      
Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ke magana a lokacin bude masallacin juma’a da ya gina a Bauchi.
Dubban jama’a ne suka halarci wannan budi masallaci cikin su manya manyan mutanen da suka halarci wannan budi masallaci har da mai martaba sarikin Bauchi injiniya Alh. Dakta Rilwanu Suleiman Adamu da kuma Galadiman Bauchi Alh. Ibrahim Saidu Jahun.
Galadiman Bauchi Alh. Ibrahim Saidu Jahun ke magana a bikin bude masallacin Jama’an wannan unguwa sunyi ta fatan alkhairi ma gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar a kan wannan aiki na gina wannan masallaci.
Al’umman musulmai a wajen bude masallacin An bude babban masallacin juma’an da gwamnan Bauchi ya gina (Hotuna) Mai martaba sarikin Bauchi injiniya Alh. Dakta Rilwanu Suleiman Adamu (tsakiya), gwamnan Bauchi da kuma Galadiman Bauchi.
           

The post YIWA ADDINI HIDIMA: GWAMNAN JIHAR BAUCHI YAYI BIKIN BUDE WANI BABBAN MASALLACIN JUMA’A DAYA GINA-HOTUNA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>