Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

MADALLA: WANI BABBAN HAMSHAKIN DAN KASUWA YA AURAR DA MATA MARAYU DA NAKASASSU 50 A JIHAR YOBE

$
0
0

Wani Babban Attajirin Dan Kasuwa Ya Aurar Da Mata Marayu Da Nakasassu 50 A Jihar Yobe.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Wani Shahararren dan kasuwa a Jihar Yobe mai suna Alhaji Mohammed Yakubu Jacob ya aurar da ‘Yan mata marayu da marasa galihu akalla su 50 a kofar fadar mai martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Sulaiman.
     
Dnadalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa wannan al’ amarin ya dauki hankulan al’umma da dama kasantuwar cewa a cikin watan da ya gabata ma wannan bawan Allah ya aurar da ‘Yan mata 40 a garin, bayan Iyaye da wasu wakilai sun kai kokensu a gare shi.
A cewar mai Martaba sarkin Bade, akasarin ‘Yan matan marayu ne da ‘Yan gudun hijira wadanda suka sami mazajen aure, amma Iyayen su ko wakilan su ba su da halin aurar da su sakamakon halin rashi.
A yanzu haka dai wannan bawan Allah ya koyar da ‘Yan matan sana’o’i daban-daban tare da basu jari domin dogaro da kai, sannan Fadar sarkin ta nada wani kwamiti da zai dinga yin sulhu a tsakanin ma’auratan dan samun kyakkyawar fahimta a rayuwarsu ta aure.

The post MADALLA: WANI BABBAN HAMSHAKIN DAN KASUWA YA AURAR DA MATA MARAYU DA NAKASASSU 50 A JIHAR YOBE appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>