Rikicin Gwamna El-rufa’i Da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Na Cigaba Da Barin Baya Da Kura..
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Rikicin Gwamna Jihar Kaduna Mallam Nasiru El-rufa’i da Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan abin sai kara gaba yake.
Kwanaki ne dai gwamnan na jihar kaduna mallam Nasir El-rufa’i yace alokacin da Jonathan yake mulkin kasar nan,yayi son zuciya ta yadda yafi fifita gwamnonin Jam’iyyar sa ta PDP da suke tare akan wasu sauran gwamnoni.
El-rufa’i ya cigaba da cewa Tsohon Shugaban kasar ya ware wasu makudan biliyoyin kudade zuwa ga jahohin da PDP take mulki a wancan lokaci amma ya hana wasu sauran jahohi.
A yanzu haka dai mai magana da yawun Jonathan Ikechukuwa Eze ya maidawa gwamna Nasir El-rufa’i martani akan furucin da yayi,Ikechukuwa Eze ya karya ta zancen da yayi a matsayin cewa malam Nasir EL-rufa’i babban makaryaci ne domin kuwa zancen rabon kudade akan ka’ida akayi babu fifiko ko nuna saniyar ware ga wata jaha ko gwamna.
The post KARANTA KAJI: WATA SABUWA RIKICI YA SAKE BARKEWA TSAKANIN GWAMNA EL-RUFA’I DA GOOGLUCK EBELE JONATHAN appeared first on MUJALLARMU.