Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Cigaba Da Rikon Hukumar EFCC Da Ibrahim Magu Yakeyi Ya Sabawa Kundin Tsarin Mulkin Kasa. Cewar Wasu Kungiyoyin Fararen Hula.

$
0
0

Gamayyar wasu kungiyoyin fararen hula Karkashin jagorancin Global Center for Conscious Living Against corruption a turance, sunyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta tumbuke shugaban riko na hukumar EFCC tare da maye gurbin shi da wanda ya dace, a cewar kungiyoyin cigaba da rikon hukumar EFCC da magu yakeyi abune wanda ya sabawa dokokin kasa kasancewar ya cika kwanaki 90 ba’a aminta dashi ba.

Dr. Gabriel Nwambu babban daraktan Global Centre for Conscious living against Corruption a turance, ya tabbatarwa manema labaru cewar baya ga karya dokar tsarin mulkin kasa, Ibrahim Magu ya nuna gazawa wajen yakar ayyukan rashawa yadda ya kamata a kasarnan.

Dr. Gabriel ya koka kan yadda hukumar ta EFCC tayi barin wasu kararrakin da ta shigar kotu inda ya dangantasu da rashin kwarewar aiki na shugaban hukumar ta EFCC. Dr Gabriel ya bukaci hukumomin da abun ya shafa cewar su hanzarta yin waje road da shugaban na hukumar EFCC sannan su maye gurbin shi da wanda ya dace.

Hajj SHehu

The post Cigaba Da Rikon Hukumar EFCC Da Ibrahim Magu Yakeyi Ya Sabawa Kundin Tsarin Mulkin Kasa. Cewar Wasu Kungiyoyin Fararen Hula. appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>