Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

BANYI FADA DA KOWA BA,TSAUSAYI NE YA FADA MIN-ADO GWANJA

$
0
0

Dandalin Kannywood:Banyi Fada Kowa Ba Tsautsayi Ne Ya Fada Min-a=Ado Gwanja.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Jarumi,kuma Mawaki
Daga Abu Aneesah Kaduna
Kwana biyu kenan ake ta raɗe raɗi a shafukan sada zumunta na yanar gizo kan wani hoto da fitaccen dan fin kuma mawaki Ado Isa Gwaja yasanya da kansa a shafukansa na sada zumunta domin sanar da masoyansa halin da yake ciki da kuma iftila’in da ya fada masa, inda yasa matsalan kunburi a gefen idonsa sakamakon wani akasi daya faru.
                                  
Ganin yadda ake ta yaɗa labarin kashi daban daban yasanya muka kira manajansa Ahmed Danja don jin gaskiya akan lamarin, kaman yadda wasu suka buga cewa ado gwanja yayi dambe ne aka gwabjeshi wasu kuma sukace ai kofa ce ta bugeshi ko windo da dai sauransu. Wakilinmu Abban Aneesa dake Kaduna a sanyin safiyan Lahadin nan ya kira Ado Gwanja bai samu wayarsa ba, sai ya kira na hannun damansa kuma Manajansa indo ko yayi sa’a ya dauka sai ya jajanta mai akan lamarin sannan ya tambayeshi ainihin hakikanin gaskiyar akan yadda ake yaɗa jita-jita, sai Ahmed Danja ya kada baki yace dafarko muna godiya da jajanta mana da kukayi, sannan kuma naji daɗin kirana da kayi domin akasari irin wannan jita-jita shi wasu ke jira sai yasa da faruwan abun Ado yace kafin wasu su sanya bari shi ya fara sawa a shafukansa na sada zumunta amman duk da haka kaga sai da wasu sukata juya labarin ta inda sukaga
yafi masu, wasu ta batanci wasu kuma ta hanyar da ba ɓatanci ba. Toh gaskiyar abinda ya faru wasu yaran Ado Gwanja yan sanda suka kama abakin studio dinsa yaje belinsu, anan yan sanda suka nemi kudi Ado yace ai beli kyauta ne, ya dauko abinda yaga zai iya ya basu suka ki amsa cikin waɗanda Ado yaje dasu sai ya fara fada akan don me za’a basu kudi suki amsa har sai abinda suke so, to anan ne wani ɗan sanda ya husata da magananshi ya dauko gora zai maka ma wanchan sai ya kauce sai goran ta samu Ado a gefen idonsa shine wannan kunburin da kagani, kaji ainihin abinda ya faru.
                                 
Da aka tambayeshi ko akwai wani mataki dasuka ɗauka akan hakan sai yace “eh mun dau mataki domin har mun gurfanar dashi ɗan sandan amman sai wasu makusantar mu suka nuna mana tunda bada niyyar dukan Ado yayi tun farko ba kuma tsautsayi bata wuce rananta kota gunshi ko ta wani hanyar hakan sai ta faru da Ado da a hakura a rabu dashi domin gudun karya rasa aikinsa ko gurfanar dashi da akayi ya hankalta tunda bashi kadai ba harda yan uwansa ke bada hakuri, sai muka janye muka rungumi kaddara.
Zanyi amfani da wannan daman domin yin kira ga masu baza ko wace irin jita-jita harda wasu kafafen yaɗa labarai wanda duk wata hanya da zasu sanemu suna da ita amman dasunga wani yace kaza don kar ace anbarsu abaya gurin kawo labarin sai kaga suma sun ma labarin kwaskwarima don Allah su taimaka mana gurin faɗin labarai nagaskiya kuma wallahi akan irin wannan lokacin kaɗan ya rage ga duk wata kafan da bata bi ka’ida ba ta yaɗa labarin karya akan mu zamu fara gurfanar da ita agaban kotu, daga karshe ina yima masoyan fatan Allaheri da kuma gode masu akan kaunar da ake nuna mana da kuma irin addu’o’in da kuke mana muna godiya matuka, muna fatan a wannan watan baza ku manta damu cikin Addu’o’in ku ba. Mungode.

The post BANYI FADA DA KOWA BA,TSAUSAYI NE YA FADA MIN-ADO GWANJA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050