Munyi kuskure game da furucin da mukayi kan yan kabilar Igbo – Gamayyar matasan Arewa.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Shugabannin kungiyar matasan arewa sunyi amai sun lashe bayan kuran da suka tayar Shugabannin sunce zasu bada daman tattauna soke-soken da akayi bisa ga furucinsu Game da cewarsu, Najeriya zata cigaba tamkar tsintsiya madaurinki daya Gamayyar kungiyoyin matasan arewa ta janye maganar da tayi na baiwa yan kabilar Igbo wa’adin kwanaki 120 domin barin arewacin Najeriya kuma da cewa dukkan yan arewan da ke garuruwansu su dawo gida.

Da yammacin jiya, shugabannin kungiyar sun shiga ganawar gaggawa domin tattaunawa bayan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai ya bayar umurnin damke wadanda sukay wannan furuci.
Gamayyar matasan Arewa tayi amai ta lashe Daga baya, kakakin gamayyar Abdulaziz Suleiman yayi bayani wa manema labarai cewa : “Ya bayyana cewa matakin da muka dauka farko ba daidai bane.
Akwai bukatan aiki tare a matsayin kasa daya. Wannan ba lokacin tattauna rabuwa bane.
Akwai bukatan hada kai. Ba’a san arewa da rashin lumana ba.”
The post KARANTA KAJI: KUNGIYAR MATASAN AREWA TAYI AMAI TA LASHE GAME DA FURUCIN KORAR KABILAR IBO DAGA YANKIN AREWA appeared first on MUJALLARMU.