Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

TSARABAR RAMADAN: FALALA 20 DAGA MALAM AMINU DAURAWA AKAN AZUMIN WATAN RAMADAN

$
0
0

Ramadan: Falala Ashirin Daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Marubuci:Haruna Sp Dansadau.

Ramadan: Falala Ashirin Daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Falala Ashirin Daga Malam Aminu Daurawa

1) A Cikinsa Aka Saukar da Alqur’ani mai girma.
Bakarah 185
2) Dukkan Littafan Allah mai girma, A cikin sa aka saukar dasu, Takardun Annabi Ibrahim A daren farko na watan, Attauran Annabi Musa a ranar 6 ga watan, Injilar Annabi Isa 13 ga watan, Alkur’ani Annabi Muhammad SAW a ranar 24 ga watan, Musnad Ahmad, Sheikh Albany ya Ingantashi .
3) Ana bude kofofin Aljannah a cikin watan.
4) Ana rufe kofofin wuta
5) Ana daure kangararrun Shedanu
6) Ana bude kofofin Rahma
7) Ana bude kofofin Sama
8) Mai kira yana kira, Ya mai neman alkhairi gabato, Ya mai neman sharri, Kayi nisa
9) A ko wane dare,  Allah yana yanta bayi daga wuta
10) A cikin watan akwai daren Lailatul Kadri Wanda Yafi wata dubu,
11) Ana kankare zunuban shekara, Annabi SAW ya ce, Daga Ramadan zuwa Ramadan ake kankare zunubai duka, Matukar an nisanci Kaba’ira
12) An durmuza hancin, Duk wanda Ramadan ya kama har ya wuce baiyi aikin da za ayi masa Rahama ba.13) Umra a cikin watan Ramadan dai dai yake da aikin Hajji tare da Annabi SAW a wajen Lada
14) Watan da aka fi shiga i’tikafiF A goman karshe
15) Watan da ake amsa addu’a
16) Watan da ake son yawaita karatu Alkur’ani mai girma, Karatun Alkur’ani mai girma, Akalla sauka hudu duk sati daya.
17) Watan alkhairi da kyauta da ciyarwa, Da samun dimbin lada, Duk wanda ya ciyar da mai azum, Zai kara samun lada kamar yayi azumi.

18) Watan da akafi yawan kiyamul laili da tarawih da tahajjud da asham don kara kusanci da Allah.
19) Watan neman nasara akan makiya.

Abubuwan da suke karya Azumi:
1: Cin abinci da gangan
2: Shan abin sha da gangan.
3: Saduwa da mace da gangan.
4: Kakaro amai da gangan
5: Fasa niyar azumi.
6: Rashin dauko niyya tun dare ga mai azumin farilla.
7: Zuwan jinin Al’ada ko na haihuwa ana cikin azumi.
8: Shafar gaba da sha’awa, Ko kallo,  Da shaawa,  Ko tunanin mace da sha’awa,  Har maniyyi ya fito.
9: Yin ridda da fita musulunci.
10: Yin Allurar abinci

Masu Shan azumi saboda larura:
Saboda Rahmar Allah, Da jin kansa, Da Tausayinsa, Da Saukakawarsa ga bayinsa, Aka sami sauki ga masu larura su sha azumi, wasu su rama, wasu su ciyar, wasu kuma babu ramuwa babu ciyarwa

1:  Mace mai jinin Al’ada, bayan ta gama sai ta rama
2: Mace mai zubar jinin haihuwa, bayan azumi sai ta rama3:  Mace mai ciki wanda ta ji tsoron kada dan cikinta ko ita su jikkita, Ta ciyar ko ta rama.
4: Mace mai shayarwa, wacce idan tayi azumi, bata iya shayarwa, bayan azumi sai ta rama ko ta ciyar
5: Tsoho ko tsohuwa, Wanda tsufa ya hana su azumi, sai su ciyar da miskini daya ga kowanne azumi.
6: Mahaukaci, babu azumi akan sa babu ramuwa.
7:  Yaro, babu azumi akan sa babu ramuwa amma a fara koya masa tun yana karami.
8:  Mara lafiya, Idan ya sha azumi sai ya rama.
9: Idan yasha azumi saboda tafiya sai ya rama bayan Ramadan.
10: Mai ciwon farfadiya, Idan ciwon ya taso yasha azumi babu ramuwa a kansa
11: Mai ciwon kishiruwa wanda baya daukan lokaci, sai yasha ruwa, babu azumi a kansa, sai ya ciyar.
12: Mai ciwon yunwa, Idan yasha azumi sai ya ciyar idan ya warke, Idan bai warke ba, sai ya ciyar albarkacin azuminsa..

Abubuwan da basa karya azumi:
Abubuwa da dama suna faruwa ga mai azumi, amma basu shafi ingancin azuminsa ba kamar yadda dalilai suka tabbatar. Ga 20 Daga Ciki.
1: Cin abinci da mantuwa
2: Shan abin sha da mantuwa
3: Saduwa da mace da mantuwa
4: Rinjayar fitar amai
5: Yin allura ta jijiya ko ta nama ko ta masu ciwon suga.
6: Bayar da gudunmawa na jini.
7: Hadiye miyau ko majina.
8: Jin rauni ko ciwo.
9: Jin kamshi turare na ruwa, ko na hayaki.
10: Sa kwalli ko tozali a ido.
11: Diga magani a kunne ko a ido, banda hanci
12: Yin aswaki ko makilin da burush, amma a kuskure baki sosai, kada zakin ya wuce.
13: Dandana abinci, amma kada a hadiye.
14: Shakar magani masu ciwon asma, domin hanyar iska yake bi.
15: Shakar kura, ko hayaki amma banda na sigari.
16: Wanda ya yi mafarki yana azumi har ya fidda maniyyi, sai yayi wanka, amma azuminsa yana nan.
17: Wanda yayi janaba da daddare amma baiyi wanka ba, sai bayan alfijir ya fito.
18: Yin wanka da jika jiki don sanyi
19: Idan wani kwaro ko guda ya shige masa baki, ya wuce zuwa ciki babu komai.
20: Idan wani yayi masa tilas ya karya azumi, ya ji tsoran ransa ya karya, babu komai azuminsa yana nan.

Sunnonin Azumi
1: Yin sahur, kuyi sahur domin acikin sahur akwai albarka Bukhari 1923 Muslim 1095I.
2: Gaggauta buda baki, Mutane ba zasu gushe ba acikin alkhairi matukar suna buda baki da zarar rana ta fadi Bukhari 1957 Muslim 1098.
3: Yin buda baki da dabino mai laushi, Idan babu sai a yi da ruwa, Abu Dauda 2358 Tirmiziy 692
4: Addu’a buda baki ذهب الظما وابتلت العروق وثبت الأجر إن شاء الله Abu Dauda 2359 Tirmiziy 3329.
5: Yawan karatun Al’qur’ani kamar yadda Annabi SAW ke yi. Bukhari Muslim .
6  Idan wani ya zageka kana azumi, ko ya nemeka da fada, kace azumi nakeyi, kada ka biye masa
7: Ka Kiyaye harshenka daga giba da karya da shedar zir.
8: Ka Yawaita istigfari da ambaton Allah.
9: Ka Kiyaye Sallah a jam’i
10:Ka Kiyaye duk abinda zai bata maka azumi

The post TSARABAR RAMADAN: FALALA 20 DAGA MALAM AMINU DAURAWA AKAN AZUMIN WATAN RAMADAN appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050